Ana Murna Magana Ta Lafa, Sanatan Amurka Yana Harin Jika wa Tinubu Aiki
- Ted Cruz ya bayyana cewa Najeriya na amfani da yakin baka wajen boye gaskiyar abin da ke faruwa
- Sanatan na Amurka ya dage cewa ba a kawo karshen matsalar muzguna wa kiristoci a kasar nan ba
- Cruz ya gabatar da kudirin doka a Majalisar Amurka don kakaba takunkumi ga jami'an gwamnatin Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
US - Ted Cruz ya soki yadda jami’an gwamnatin Najeriya suka fuskanci lamarin zargin kashe da muzguna wa kiristoci.
Sanatan na Amurka bai lafa daga suka ba har yanzu, bai ji dadin yadda gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta tunkari matsalar ba.

Source: Getty Images
Sanata Ted Cruz ya yi magana a X
Sanata Ted Cruz ya zo shafinsa na X a ranar Laraba 23 ga watan Yuli 2026, yana magana game da abin da ke faruwa a Najeriya.
Majalisar Amurka ta yi magana a kan halin da ake ciki a Najeriya, don haka ne Ted Cruz ya tofa albarkacin bakinsa a shafinsa.
‘Dan majalisar ya zargi gwamnatin kasar nan da bada dama a rika yi wa kiristoci da sauran addinai kisan gilla ta hanyar kafa dokokin sabo da shari’a kuma sun kyale masu tsaurin ra’ayin addini sun ta’adi.
"Gwamnatin Amurka ta san jami’an gwamnatin Najeriya da ke da hannu a wannan tsare-tsare
"Na yi ta kokarin gabatar da kudiri a hukunta su, kuma har Shugaban kasa Trump ya yi umarni a dauki matakin soji."
- Ted Cruz
Gwamnati ta dauko salon yakin baka
The Cable ta rahoto Cruz yana cewa a maimakon a shawo kan al’amarin, sai gwamnati ta maida shi salon yakin baka.
Maimakon su maida hankali a kan koken Amurkan, jami’an Najeriya sun fito sun dauko salon yaki da masu sukarsu.
Fitaccen ‘dan siyasar yana ganin gwamnati ta manta da jaki ne an tafi ana dukan mangala.

Source: Getty Images
A lokuta dabam-dabam, Gwamnatin Najeriya ta fito ta karyata zargin muzgunawa kiristoci, ta ce ba haka abin yake ba.

Kara karanta wannan
Da gaske gwamnatin Tinubu ta karbo bashin Naira tiriliyan 80? Minista ya yi martani
Ted Cruz wanda yake tare da jam’iyya mai mulki a Amurka ya ce Gwamnatin Najeriya ba ta da niyyar canza yadda abubuwa suke tafiya.
Amma a cewarsa, Fadar White House ta Amurka ba ta tare da jami’an na Najeriya a karkashin Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya soma yakar Bola Tinubu
Aikin Atiku Abubakar ya soma aiki a Amurka, domin an ji labari an kai wa Donald Trump tsegumin wasu sirrorin Bola Tinubu na shekaru.
Kamfanin Von Batten-Montague-York da Atiku Abubakar ya ɗauki hayarsa kan $1.2m ya saki tsofaffin takardun shari’ar Tinubu a Amurka.
A kokarin bata wa shugaban na Najeriya suna, an ji yadda Von Batten-Montague-York ya zauna da wasu 'yan majalisar kasar Amurkan.
Asali: Legit.ng
