Shirin Amurka na Samar wa Saudi Nukiliya Ya Firgita 'Yan Isra'ila
- Yarjejeniyar nukiliyar da Amurka da Saudiyya suka cimma ta tayar da hankula a Isra'ila kan yiwuwar barkewar gasar mallakar makaman a yankin
- Tsofaffin shugabannin Isra'ila sun gargadi cewa shirin zai iya jefa yankin cikin sabon rikici tare da barazana ga tsaron ƙasar
- Yarjejeniyar za ta bai wa Saudiyya damar gina tashoshin makamashin nukiliya tare da tace sinadarin uranium domin shirin samar da makamashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tel Aviv – Yarjejeniyar da Amurka da Saudiyya suka cimma domin bai wa masarautar damar gina tashoshin makamashin nukiliya ta amfani da fasahar Amurka da kuma tace sinadarin uranium ta haifar da fargaba a Isra'ila.
Rahoto ya nuna cewa yarjejeniyar, wacce har yanzu ke jiran amincewar Majalisar Dokokin Amurka, an tsara ta ne domin taimaka wa Saudiyya ta bunƙasa shirin makamashin nukiliya na farar hula.

Source: Getty Images
Sai dai, Reuters ta wallafa cewa masu suka a Isra'ila na ganin cewa matakin zai iya zama barazana ga tsaron ƙasar a nan gaba.
Korafin 'yan Isra'ila
Tsohon Firaministan Isra'ila, Naftali Bennett, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban kuskuren dabarun tsaro wanda zai iya jefa Isra'ila cikin haɗari.
Ya ce ba da damar tace uranium a cikin ƙasar Saudiyya na iya haddasa gasar mallakar makaman nukiliya a Gabas ta Tsakiya tare da rage ikon da ake da shi wajen dakile yaɗuwar irin waɗannan makamai.
Bennett, wanda ke neman kayar da Firaminista Benjamin Netanyahu a zaɓen da za a yi ranar 27 ga Oktoban 2026, ya ce ya kamata Isra'ila ta ɗauki matakin dakatar da yarjejeniyar.

Source: Getty Images
Lieberman ya yi gargaɗi
Shi ma tsohon Ministan Tsaron Isra'ila, Avigdor Lieberman, ya yi zargin cewa shirin makamashin nukiliya na farar hula a Saudiyya na iya kaiwa ga mallakar makaman nukiliya.
Al Jazeera ta wallafa cewa ya ce hakan zai iya haddasa wata mummunar gasar mallakar makaman nukiliya a duk faɗin Gabas ta Tsakiya.
Lieberman ya ce wajibi ne Isra'ila ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen jan hankalin Majalisar Dokokin Amurka domin hana amincewa da yarjejeniyar.
Bayani kan yarjejeniyar
Rahotanni sun nuna cewa tun zamanin mulkin shugaban Amurka Donald Trump na farko da kuma gwamnatin Joe Biden ake tattaunawa kan wannan yarjejeniya.
Sai dai kungiyoyin da ke adawa da yaɗuwar makaman nukiliya sun dade suna gargadin cewa shirin na iya ba Saudiyya damar mallakar makaman nukiliya a nan gaba.
An nemi kama Netanyahu
A wani labarin, mun ruwaito cewa magajin garin birnin New York, Zohran Mamdani, ya bukaci gwamnatin tarayyar Amurka ta aiwatar da sammacin kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.
Mamdani ya bayyana Netanyahu a matsayin wanda ake zargi da aikata laifukan yaƙi, yana mai cewa duk da New York ba ta da ikon kama shi, gwamnatin tarayya na da ikon aiwatar da hakan.
An nemi a cafke Benjamin Netanyahu ne saboda kashe fararen hula ciki har da yara kanana da ya rika yi a yankuna Falasdinawa a Gaza.
Asali: Legit.ng

