Yan Majalisa a Amurka Sun Haɗa Kai domin Hana Trump Ci Gaba da Yaƙi da Iran

Yan Majalisa a Amurka Sun Haɗa Kai domin Hana Trump Ci Gaba da Yaƙi da Iran

  • Majalisar Wakilai ta Amurka ta taso da karfi domin kada kuri'ar umurtar Shugaba Donald Trump ya dakatar da yakin Iran
  • Mambobin Majalisar Dattawa sun kasa amincewa da irin wannan kuduri, yayin da rikicin Iran ke kara tsananta tare da karin kashe-kashen sojojin Amurka
  • Majalisar ta ce Trump bai nemi amincewar Majalisa ba kafin yakin, yayin da gwamnati ke neman karin kudaden gudanar da yakin da kasafin Pentagon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Majalisar Wakilai ta Amurka ta kada kuri'a domin umurtar Shugaba Donald Trump.

An kada kuri'a musamman domin dakatar da Trump ya kawo karshen yakin da ake yi da Iran.

Trump yana fuskantar barazana game da yaki da Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Kudurin ya samu goyon bayan 'yan Democrat tare da 'yan Republican hudu da suka saba wa matsayar jam'iyyarsu, cewar CBS News.

Kara karanta wannan

PFIPC: Atiku ya ba majalisa mafita bayan CBN da Akanta janar sun yi baki 2

Ana shirin taka wa Trump birki

Kudurin, wanda 'yar majalisa Pramila Jayapal ta gabatar, ya bukaci shugaban kasa ya janye dakarun Amurka daga duk wani farmaki ko aikin soja da ake yi kan Iran, ciki har da yiwuwar tura sojojin kasa domin fada ko mamaya, sai idan Majalisa ta bayar da takamaiman izini.

'Yan Republican da suka goyi bayan kudurin sun hada da Tom Barrett na Michigan, Brian Fitzpatrick na Pennsylvania, Warren Davidson na Ohio da Thomas Massie na Kentucky, wadanda suka rabu da ra'ayin mafi yawan jam'iyyarsu.

An gudanar da kuri'ar ne bayan wasu sojojin Amurka sun mutu sakamakon hare-haren Iran a yankin, yayin da kudin yakin ke ci gaba da karuwa ba tare da alamar kawo karshensa ba.

Shugaba Trump ya yi watsi da damuwar wasu 'yan majalisar musamman Republican game da illar siyasar yakin, musamman yadda zai iya shafar zaben tsakiyar wa'adi, duk da cewa mafi yawan jam'iyyar na ci gaba da goyon bayan yakin.

Kara karanta wannan

ADC ta nemi gwamnati ta fito da bayanai kan yadda aka kashe N17.5tr a NNPCL

Jayapal da Jason Crow sun bayyana wa 'yan Democrat cewa yana da matukar muhimmanci Majalisa ta kare ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta wajen yanke hukunci kan shiga yaki.

Trump na fuskantar matsala a yaki da Iran
Shugaba Donald Trump yayin taron karbar gawar daya daga cikin sojojin da suka mutu a yaƙi Iran. Hoto: Kevin Dietsch.
Source: Getty Images

Abin da Trump ya ce ga majalisa

A ranar 10 ga Yuli, Trump ya sanar da Majalisa cewa an sake fara aikin soja kan Iran bayan ya bayyana cewa tsagaita wutar wata guda da aka yi ta kare, cewar NBC News.

Gwamnatin Trump ta ce lokacin da aka dakatar da rikicin a watan Afrilu ya sake kunna wa'adin kwanaki 60 da dokar War Powers Resolution ta tanada, duk da cewa tana ganin wannan sashe na dokar bai dace da kundin tsarin mulki ba.

A watan da ya gabata, Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa sun amince da kudurin da ke takaita ikon Trump na ci gaba da daukar matakin soja kan Iran ba tare da izinin Majalisa ba.

'Yan Democrat sun ce suna nazarin hanyoyin shari'a domin tilasta shugaban kasa bin kudurin, tare da shirin hana karin kudaden yakin ta hanyar tsarin kasafin kudi.

Gwamnatin Trump ta nemi karin dala biliyan 67 domin biyan kudin yakin da sake cike kayan aikin soja, sannan tana neman dala tiriliyan 1.5 domin kasafin Pentagon na shekarar kudi mai zuwa.

Kara karanta wannan

An taso Tinubu a gaba game da lafiyarsa kan sake neman takara a 2027

Sharudan Trump ga Saudiyya game da Isra'ila

An ji cewa shugaba Donald Trump ya ce yarjejeniyar makamashin nukiliyar Amurka da Saudiyya za ta tabbata ne idan Riyadh ta amince da Isra'ila.

Trump ya jaddada cewa Saudiyya ba za ta riƙa tace sinadarin uranium ba, yana mai cewa shirin ya shafi amfani da makamashin nukiliya.

Saudiyya ta sha bayyana cewa ba za ta amince da Isra'ila ba sai an kafa ƙasar Falasdinu, yayin da Isra'ila ta yaba da sabon sharadin Trump.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.