An Ayyana Neman Wani Sojan Najeriya Ruwa a Jallo, An Saki Hotuna da Bayanansa
- Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana wani soja da ake zargi da sayar wa ‘yan ta’adda kayan soji a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo
- Ana zargin Private Mohammed Yusuf Amutu da sayar da kayan soji ga ‘yan ta’adda da masu aikata laifuffuka
- Rundunar ta ce ta fara farautar sojan bayan ya tsere daga sansaninsa tun watan Yuni yayin da aka nemi jama'a su taimaka wajen cafke sojan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Rundunar Nigerian Army Ordnance Corps (NAOC) ta ayyana wani daga cikin jami'anta, Private Mohammed Yusuf Amutu, a matsayin wanda ake nema bisa zargin hannu wajen sayar da kayan soji ga 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa ana zargin sojan da sayar da kayan soji, musamman kayan sanye na rundunar, ga 'yan ta'adda da wasu miyagu.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: An yanke wa mutum 3 hukuncin daurin rai da rai kan sace daliban Oyo

Source: Twitter
Sojan ya tsere daga sansaninsa
Oluwatope Dorcas Aluko, mataimakiyar daraktar hulda da jama'a ta hedikwatar sojojin kasan Najeriya ta fitar da sanarwar da aka wallafa a shafin rundunar na X a ranar 23 ga Yulin 2026.
Rundunar ta ce Mohammed Yusuf Amutu yana aiki ne a Nigerian Army Ordnance Kits Factory, amma ya tsere daga sansaninsa tun ranar 3 ga Yunin 2026.
Bayan guduwar tasa, hukumomin soja sun ayyana shi a matsayin wanda ake nema, yayin da aka fara gudanar da bincike da kuma farautarsa domin cafke shi.
Sanarwar ta ce idan aka kama shi, za a gudanar da cikakken bincike tare da daukar matakin ladabtarwa da ya dace bisa dokokin rundunar soja.
An yi gargadi kan taimaka wa 'yan ta'adda
NAOC ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani nau'in rashin da'a ko laifi da zai iya kawo cikas ga aikin rundunar ko kuma barazana ga tsaron kasa ba.
Ta ce duk wani jami'in soja da aka samu da laifin sayarwa, karkatarwa ko bai wa 'yan ta'adda kayan soji ko wasu kayayyakin gwamnati ba tare da izini ba, zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa dokokin soja da na farar hula.

Source: Twitter
An bukaci jama'a su taimaka
Rundunar ta kuma yi kira ga jama'a da su taimaka da sahihan bayanai da za su kai ga cafke sojan da ake nema.
Ta bukaci duk wanda ke da wani bayani game da inda yake ya sanar da sansanin soja mafi kusa ko kuma duk wata hukuma ta tsaro.
A cewar sanarwar, rundunar za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya, kwarewa da kuma kare dukkan kayan aikin soja, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Sojojin da ake nema sun tsallake ketare
A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa jami’ai biyu sun tsere bayan sun shiga cikin jerin wadanda ake zargi da shirin juyin mulki.
Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an da suka tsere sun hada da wani Manjo daga jihar Taraba da kuma daya daga birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa sama da jami’an soja 30 yanzu suna tsare da ake bincike kan zargin juyin mulki wanda ya ta da hankula a kasar.
Asali: Legit.ng
