Auren Ƴan Fim: Amaryar TikTok Ta Fadi Matsalar da Jaruman Kannywood ke Fuskanta
- 'Yar wasan Kannywood, Hafsat Tuge, ta yi magana kan kallon da ake yi wa 'yan fim mata a matsayin wadanda ba su dace da aure ba
- Wacce aka fi sani da Amaryar TikTok, ta ce 'yan matan Kannywood suna zaman aure kuma suna girmama mazajensu, akasin tunanin mutane
- Amma da aka tambaye ta lokacin da za ta yi aure, Hafsat ta bayyana cewa aure yana da lokacinsa, amma a ba shi ne a gabanta yanzu ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Shahararriyar ƴar wasan Hausa, Hafsat Tuge, ta fito ta yi martani kan ikirarin da ake yi na cewa jaruman Kannywood "ba matan da za a aura ba ne."
Ba wannan ne karon farko da aka samu wata jaruma a Kannywood ta kare ikirarin ba, sai dai, har gobe, ana yi wa ƴan fim din kallon matan da zaman aure ke masu wahala.

Asali: Facebook
"Jaruman Kannywood na aure" - Hafsah Tuge
A hirar ta da BBC Pidgin, Hafsat Tuge, wacce ta aka fi sani da Amaryar TikTok ta ce ƴan matan Kannywood na zaman aure, kuma suna girmama mazajensu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarta, kuskuren fahimta ne kawai ke sanya mutane su rika kallon ƴan fim a matsayin matan da ke kashe aurensu ko su ma ki yin auren da gangan.
Jaruma Hafsat Tuge ta ce:
"Muna yin aure, kuma muna zaman aure, kawai dai yanayin al'ummar da muke rayuwa a cikinta ne ya sa ake ganin kamar ba ma auruwa.
"Mutane ne kawai ke mana kallon kamar ba ma girmama mazajenmu, saboda muna samun kuɗi, muna mu'amala da maza. Kuma ba haka ba ne, mu ma kamar sauran mata ne."
"Aure ba ya gabana yanzu" - Amaryar TikTok
Hafsat Tuge dai ta shahara a masana'antar Kannywood tun bayan da ta fito a wani fim mai suna Amaryar TikTok, wanda a karshe ya zama kamar inkiyarta.
Da aka tambaye ta lokacinta da take ganin za ta yi aure, Hafsat Tuge ta ce:
"Zan yi aure idan lokaci ya yi. Ka san shi aure lokaci ne idan lokacin ya zo, to zan yi aure. Amma a yanzu dai, babu aure a gabana yanzu."
Ko da aka tambaye ta, jaruman Kannywood na lalata tarbiya? Amaryar TikTok ta ce:
"Kowa na kallon fim, kuma idan ka ce abin da ka ga an yi a fim shi za ka yi, to kana cikin matsala. Fim ba gaskiya ba ne.
Game da ko jarumai mata sun fi saurin samun daukaka a kan jarumai maza, Amaryar TikTok ta ce komai lokaci ne, kuma Allah ne ke ba da daukakar.

Asali: Facebook
Mutum na bukatar ubangida kafin ya yi nasara?
A cewarta, duk iya kokarin da jarumi zai yi, ba zai iya samawa kansa daukaka ba, dole ya jira lokacin da Allah ya tsara masa.
Hakazalika, ƴar wasan Hausan ta ce akwai jarumai da dama da suka daukaka ba tare da sun yi riko da wani ubangida ba.
Amma akwai jaruman da sai da suka jingina da wani ne suka daukaka, don haka take ganin ubangida na takara rawa wajen samun nasara, amma ba shi ne ke ba da nasarar ba.
Jarumar ta nemi gaba ɗaya ƴan Kannywood da su hada kansu, su zama tsintsiya madaurinki daya, domin samar da ci gaba da hadin kai mai dorewa a masana'antar.
'Ba ni da ubangida' - Abdul M Shareef
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Abdul M Shareef ya ce ba shi da wani uban gida a wannan masana'antar ta Kannywood.
A zantawarsa da Legit Hausa, Abdul M Shareef ya ce:
"Ni ba ni da ubangida, babu wanda ya rike hannu na ya shigar da ni fim, ko ya yi mun wani abu da ubangida ke yi wa yaransa don su daukaka a fim.
"Na sha ta yin tafiyar kasa domin na je inda ake daukar fim, babu wanda ya sanni, ban san kowa ba, amma a hankali, na fara samun karbuwa, har Allah ya kawo ni inda nake yanzu."
Sai dai Abdul M Shareef ya ce a duk inda mutum ya samu kansa, yana haduwa da wasu mutane da suke taimaka masa, walau da shawarwari, aiki, kudi ko hanya, wadanda suna taka rawa wajen samun nasarar mutum.
Abin da ya sa ake tsoron auren 'yan fim
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jarumar shirin Dadin Kowa, Fati Nayo (Kyauta Dillaliya) ta bayyana cewa mazaje a kasar Hausa suna tsoron auren matan da suka waye.
Kyauta Dillaliya ta kuma ce irin yanayin da jarumai mata suke fitowa a fim shi ma ya kan sa maza su rika yi musu shedar da ba haka halinsu ya ke a zahiri ba.
Jarumar ta shawarci mazajen da ke kaunar su da aure da su rika mika masu tayin soyayyarsu ba tare da wani shakku ba, tana mai cewa matan fim sun iya rike miji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng