Dambarwar Neman Sakin Matar Gwamna Abba Ta Jefa Wasu Mutane cikin Matsala, an Samu Bayanai
Rahotanni sun ce an kama jami’an tsaro uku da ke aiki tare da matar Gwamna Abba Yusuf bayan ta bar gidan mijinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Zainab, ’yar tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso, ta shigar da ƙarar neman saki a wata kotun Abuja
Rikicin auren na faruwa ne a daidai lokacin da Abba Kabir Yusuf da Kwankwaso ke fama da saɓanin siyasa bayan gwamnan ya koma APC.
Jihar Kano - Rikicin sakin auren Gwamnan Kano, Abba Yusuf, da matarsa Zainab, ya kai ga rahotannin kama jami’an tsaro uku da ke aiki tare da matar gwamnan.
An ce kamen ya biyo bayan barin gidan mijinta da Zainab ta yi sakamakon lalacewar zamantakewarsu, lamarin da ya kai ga shigar da ƙarar neman saki a gaban wata kotun Abuja.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Zainab, ’yar tsohon gwamnan Kano kuma tsohon abokin siyasar mijinta, Rabiu Kwankwaso, ce ta shigar da ƙarar mai lamba CV/97/26.
An shigar da ƙarar ne kusan shekaru 20 bayan aurensu.
An ce kotu ta gayyaci gwamnan
Wani mamba a ƙungiyar siyasar Kwankwasiyya ya tabbatar wa jaridar The Punch cewa ana gudanar da shari’ar sakin auren.
Ya ce an aika wa Gwamna Abba Yusuf sammaci domin ya bayyana a gaban kotun ranar Talata, 17 ga Nuwamba.
Ya ce: “Eh, gaskiya ne. Matar ta bar gidan mijinta, kuma an buƙaci gwamnan ya bayyana a gaban kotu ranar 17 ga Nuwamba. Ita ce ta san dalilin da ya sa take neman sakin auren; ba na son yin hasashe.
“Tana zaune ne a Abuja, kuma lokaci zuwa lokaci take zuwa Kano. Amma an gaya mini cewa ta bar gidan mijinta kusan makonni uku da suka wuce.” In ji majiyar.
Da aka tambaye shi game da rahoton kama jami’an tsaron da ke tare da Zainab, aminin Kwankwaso ya ce yana da masaniya kan lamarin.
Sai dai wakilin jaridar ya ce bai samu damar tabbatar da kamen da kuma ainihin yadda lamarin ya faru ta wata hanya mai zaman kanta ba.
’Yan sanda sun ƙi yin tsokaci
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ƙi yin tsokaci kan lamarin, yana mai cewa tuni aka kai batun gaban kotu.
“Ba za mu iya yin tsokaci kan lamarin ba saboda tuni yake gaban kotun shari’a.” In ji shi.
Ya ƙara da cewa rundunar a matsayinta na hukuma mai sanin ya kamata, ba ta tattauna batutuwan da ke gaban kotuna.
Haka kuma, ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar Kano bai yi nasara ba, domin kwamishinan yaɗa labarai, Sanusi Bature bai amsa kiran wayar da aka yi masa domin jin matsayinsa kan lamarin ba.
Asali: Legit.ng

