Seyi Tinubu ya yi magana kan shiga hurumin Ubangiji kan tazarcen mahaifinsa

Seyi Tinubu ya yi magana kan shiga hurumin Ubangiji kan tazarcen mahaifinsa

  • Seyi Tinubu ya musanta wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke cewa babu abin da zai hana mahaifinsa kammala wa'adin shekaru takwas
  • Ɗan shugaban ƙasar ya kai ƙarar waɗanda suka ƙirƙira tare da yaɗa hoton saƙon ga rundunar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro
  • Seyi ya bayyana cewa zai ɗauki matakin shari'a kan duk wanda aka samu da hannu wajen ƙirƙira da yaɗa kalaman da ake danganta masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, ya fito ya musanta wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka danganta da shi kan wa'adin mulkin mahaifinsa, Bola Ahmed Tinubu.

Saƙon da aka wallafa a matsayin hoton sanarwa a kafafen sada zumunta ya nuna ana cewa babu wani abu da zai iya hana shugaban ƙasar kammala wa'adin mulkinsa na shekaru takwas, har da ikon Allah.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC na shirin murabus daga muƙaminsa kafin zaɓen 2027? Gaskiya ta fito

Seyi Tinubu ya wanke kansa
Seyi Tinubu da mahaifinsa, Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Instagram

Tazarcen Tinubu: Seyi ya wanke kansa

Sai dai Seyi ya bayyana cewa bai taɓa furta irin waɗannan kalamai ba, yana mai zargin cewa an ƙirƙiri saƙon ne domin bata masa suna tare da jawo fushin jama'a kan mahaifinsa, cewar Punch.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ɗan shugaban ƙasar ya jaddada cewa babu gaskiya a cikin kalaman da ake danganta masa.

Ya ce:

"Ina son bayyana karara ba tare da wata shakka ba cewa ban taɓa furta irin wannan magana ba."

Seyi Tinubu ya kai ƙarar waɗanda suka ƙirƙiri saƙon

Seyi ya bayyana cewa tuni ya kai rahoton lamarin ga rundunar 'yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa.

Ya ce ana gudanar da bincike domin gano mutanen da suka ƙirƙiri hoton saƙon tare da waɗanda suka taimaka wajen yaɗa shi a kafafen sada zumunta.

Ya kuma yi barazanar ɗaukar matakin shari'a kan duk wanda bincike ya tabbatar yana da hannu wajen ƙirƙira ko yaɗa wannan saƙo.

Kara karanta wannan

‘Dan takara bai rike sirri ba, ya fadi tanadin da ‘yan adawa suke yi wa shugaba Tinubu

An soki Seyi kan zarginsa da wasu kalaman saɓo
Dan shugaban kasar Najeriya, Seyi Tinubu. Hoto: Seyi Tinubu.
Source: UGC

Abin da Seyi ya ce kan ikon Allah

Da yake magana kan ɓangaren addini na kalaman, Seyi ya bayyana cewa samun mahaifinsa a matsayin shugaban Najeriya ya kasance bisa ikon Allah Maɗaukakin Sarki.

Ya jaddada cewa Allah ne kaɗai ke da ikon tsara al'amuran ɗan Adam, yana mai cewa babu wani mutum da zai iya yin fito-na-fito da ikon Mahalicci.

Ɗan shugaban ƙasar ya ce kalaman da aka danganta masa sun saɓa wa imaninsa da kuma yadda yake kallon ikon Allah, cewar Vanguard.

Haka kuma, ya yi kira ga 'yan siyasa da magoya bayansu da su daina amfani da ƙiyayya, yaɗa labaran ƙarya da farfagandar siyasa wajen kai wa juna hari.

Ya kuma yi gargaɗin cewa bai kamata mutane su fake da amfani da asusun da ba a san masu shi ba a kafafen sada zumunta domin ɓata sunan wasu ko cimma muradun siyasa ba.

Shehu Sani ya magantu kan sarautar Seyi

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da zai sa Obi ya gudu a Najeriya ko ya ci zaben 2027

A wani labarin, an ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci sarakunan gargajiya su guji bai wa masu rike da mukaman gwamnati sarautu.

Gargadin nasa na zuwa ne bayan Sarkin Gwandu ya nada Seyi Tinubu, dan Shugaba Bola Tinubu, sarautar Dan Zakin Gwandu a jihar Kebbi.

A nasa bangaren, Shugaba Tinubu ya taya dansa murna, yana mai cewa sarautar na zuwa da nauyin da ya kamata ya sauke cikin kankan da kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.