Trump zai Tafi China, zai Gana da Xi Jinping da Putin kan Iran da Sauransu

Trump zai Tafi China, zai Gana da Xi Jinping da Putin kan Iran da Sauransu

  • Rahotanni sun nuna cewa shugabannin Amurka, Rasha da China za su gana a birnin Shenzhen na China a mako mai zuwa
  • Donald Trump ya shirya tattauna batun rage makaman nukiliya da kuma yakin Iran da Xi Jinping da Vladimir Putin
  • Sai dai wasu jami’an Amurka sun ce ba a sa ran Donald Trump zai tattauna yakin Ukraine da shugabannin biyu a taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China – Shugabannin Amurka, Donald Trump, Rasha, Vladimir Putin, da China, Xi Jinping, za su gudanar da taron farko na hadin gwiwa tsakanin kasashen uku a birnin Shenzhen na China a mako mai zuwa.

Fadar White House ce ta sanar da hakan a ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa shugabannin za su gana ne a gefen taron kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin Asiya da Pacific (APEC).

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi martani kan rahoton kai wa tawagar Tinubu hari

Xi Jinping da Donald Trump
Xi Jinping a hagu da Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton BBC ya nuna cewa mai magana da yawun Fadar White House, Olivia Wales, ta ce taron zai gudana ne a ranar Alhamis.

Batutuwan da za su tattauna

Jami’an Amurka sun ce Trump na son tattauna batun rage yawan makaman nukiliya a duniya yayin ganawar shugabannin uku.

Wales ta ce Trump na ganin yawaitar makaman nukiliya abu ne mai matukar hadari ga duniya da rayuwar dan Adam.

Wani babban jami’in Amurka da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa Trump zai kuma tattauna batun yakin Iran da shugabannin China da Rasha.

Al Jazeera ta ce wani rahoto ya nuna cewa ba a sa ran shugaban Amurkan zai kawo batun yakin Ukraine a wannan ganawa ba.

Jami’in ya ce Amurka na da wata hanya ta daban ta tattaunawa da Ukraine da Rasha domin kawo karshen yakin, don haka ba ta ga dacewar shigar da China cikin wannan batu a taron ba.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: 'Yan bindiga sun rutsa 'yan gudun hijira a hanyar zuwa gona

Taron na iya tunawa da Yalta1945

Taron Shenzhen ya tuna wa duniya da taron Yalta na shekarar 1945, wanda shugabannin Amurka, Birtaniya da Tarayyar Soviet suka gudanar bayan yakin duniya na biyu.

A wancan lokacin, Franklin D. Roosevelt, Winston Churchill da Joseph Stalin sun tattauna tsarin zaman lafiya da sababbin iyakokin kasashe a Turai.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya nuna damuwa cewa taron na Shenzhen na iya zama kamar na Yalta, inda manyan kasashe za su sake raba yankunan da suke da tasiri a kai.

Trump zai gana da Xi

Bayan taron shugabannin uku, Trump zai kuma gudanar da ganawar aiki da cin abincin rana tare da shugaban China, Xi Jinping, a ranar Alhamis.

Wannan zai zama karo na hudu da shugabannin biyu suka gana tun bayan komawar Trump kan karagar mulki a shekarar da ta gabata.

Xi Jinping da shugaba Putin
Xi Jinping na gaisawa da Vladimir Putin. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta yi maraba da Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya jaddada bukatar karfafa alakar tattalin arziki, siyasa da al’adu tsakanin kasarsa da Najeriya.

Kara karanta wannan

Da gaske shugaban INEC ya yi amfani da shafinsa na X wajen tallata Tinubu? Gaskiya ta bayyana

Pezeshkian ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi takardun shaidar jakadancin sabon jakadan Najeriya a Iran, Ambasada Hamza Sallau, a birnin Tehran.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Oluwafemi Adeniyi, ne ya bayyana hakan, inda ya ce Iran na son gano damammakin da za su karfafa alakar kasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng