Shugaban INEC na Shirin Murabus daga Mukaminsa kafin Zaben 2027? Gaskiya Ta Fito

Shugaban INEC na Shirin Murabus daga Mukaminsa kafin Zaben 2027? Gaskiya Ta Fito

  • Hukumar zaɓe ta INEC ta ce rahoton da ke cewa shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, zai yi murabus ƙarya ne kuma an ƙirƙire shi
  • Hukumar ta buƙaci ’yan Najeriya su yi watsi da labarin tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba
  • Masu zanga-zanga sun fuskanci Amupitan a wajen Chatham House ranar Alhamis, suna neman ya yi murabus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta musanta wani rahoto da aka yaɗa a kafafen sada zumunta da ke cewa shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, na shirin yin murabus daga muƙaminsa.

Hukumar ta bayyana iƙirarin, wanda aka yaɗa tare da hoton da ke ɗauke da labarin a intanet, a matsayin ƙirƙirarren bayani da aka shirya domin yaudarar jama’a.

Amupitan.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Shugaban INEC na shirin ajiye aiki?

Kara karanta wannan

INEC ta saka ranar zaben shugaban kasa na gwaji a Najeriya

INEC ta bayyana matsayarta ne a ranar Asabar ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta buƙaci ’yan Najeriya da su yi watsi da rahoton tare da guje wa yaɗa duk wani bayani da ba a tantance sahihancinsa ba.

A cikin sanarwar, hukumar INEC ta jaddada cewa babu gaskiya a cikin iƙirarin da ake yaɗawa game da shirin shugaban nata na yin murabus.

“Wannan iƙirari ƙarya ne, an ƙirƙire shi kuma yana yaudarar jama’a,” in ji hukumar.

Ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa samun sahihan bayanai daga hanyoyin sadarwa na hukuma na INEC maimakon dogaro da saƙonnin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba tare da tantance sahihancinsu ba.

“Ana kira ga jama’a da su yi watsi da wannan ƙirƙirarren rahoto, su guji yaɗa bayanan da ba a tantance ba, sannan su riƙa dogaro da hanyoyin sadarwa na hukuma na INEC kawai domin samun sahihan bayanai.
“A daina yaɗa labaran ƙarya,” in ji sanarwar.

Masu zanga-zanga sun nemi ya yi murabus

Musanta rahoton na zuwa ne bayan da shugaban INEC ya fuskanci zanga-zanga a wajen cibiyar Chatham House da ke Landan ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa masu zanga-zangar sun tare Amupitan yayin da yake barin wani taron tattaunawa kan shirye-shiryen Najeriya na gudanar da zaɓen 2027.

Masu zanga-zangar sun kewaye motar da yake ciki, inda wasu daga cikinsu suka buƙaci ya fito domin ya saurari ƙorafe-ƙorafensu.

INEC.
Tambarin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Sun kuma yi kira gare shi da ya yi murabus bisa zargin samun matsaloli a rajistar masu zaɓe, waɗanda a cewarsu ke nuna gazawa wajen tabbatar da ingancin bayanan masu zaɓe.

Sai dai rahoton da INEC ta musanta a wannan karon shi ne wanda ke iƙirarin cewa Amupitan ya riga ya yanke shawarar barin muƙaminsa.

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa shugaban nata yana daram a mukaminss, kuma ta bayyana labarin a matsayin ƙarya.

Shugaban INEC ya taba tallar Tinubu?

Kun ji cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya musanta mallakar shafi a dandalin X da ake zargin ya yi amfani da shi wajen tallata Shugaba Bola Tinubu da APC.

Amupitan ya kuma bayyana cewa an kai batun ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ofishin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, sannan an samu rahoto daga wani bincike mai zaman kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262