Daga Yi wa Jam’iyyar APC Kamfe Mawaki Ya Tashi Barci Ya Ga An Turo Masa N100m
- Mawaki a Najeriya, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, ya ce an tura masa Naira miliyan 100 a dalilin jam'iyyar APC
- Tauraron ya yi iƙirarin cewa kuɗin ya fito ne bisa marnin Sanata Solomon Adeola, wanda aka fi sani da Yayi mai takarar gwamnan Ogun
- Sai dai har yanzu ba a tabbatar da sahihancin ikirarin ba, domin babban attajirin da aka ce shi ya aiko masa da miliyoyin bai ce komai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ogun - Shahararren mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, ya yi iƙirarin cewa ya samu kuɗi daga tallar APC.
Mista Habeeb Okikiola ya shaida wa duniya ya samu Naira miliyan 100 bayan shiga wasu ayyukan yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC mai mulki.

Source: Twitter
Tallar APC ta sa Portable ya samu kudi
Mawakin da ya shahara da salon waƙoƙin titi, ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta irinsu YabaleftOnline a X.
A cikin bidiyon, Portable yana sanye da rigar APC, tare da hula mai ɗauke da sunan Solomon Adeola, wanda aka fi sani da Yayi a siyasar Ogun.
Ya kuma nuna wasu kayan kamfen da ke ɗauke da hoton ɗan siyasar mai takarar gwamna a Ogun.
Portable ya tashi daga barci ya ga N100m
Fitaccen mawakin mai shekara 34 ya yi iƙirarin cewa bayan tashi daga barci, sai ya tarar da an tura masa Naira miliyan 100 a cikin asusunsa na banki.
Ya ce kuɗin sun zo ne bisa umarnin ɗan siyasar domin yaba masa bisa gudummawar da ya bayar a harkokin kamfen yayin da yake neman gwamna.
Da yake magana, ya nuna Alhaji Ibrahim Egungbohun wanda aka fi sani da IBD Dende ne ya tura miliyoyin a madadin sanatan Ogun ta yamma.
Ya ce:
"Masoyana! Na tashi daga barci sai na tarar da saƙon shigar Naira miliyan 100 daga Yayi!

Kara karanta wannan
‘Dan takara bai rike sirri ba, ya fadi tanadin da ‘yan adawa suke yi wa shugaba Tinubu
IBD Dende, shugabana! Allah ya saka maka da alheri. Na gode!
Da farko mawakin bai san zai samu kudi ba
Daily Post ta rahoto cewa tauraron ya yi wa jam’iyyar APC aikin kamfe a baya, amma ba a biya shi ba, sai wannan karo kakarsa ta yanke saka da kyau.
Yake cewa da ya tashi barci, sai ya tuna cewa IBD ya ce ya koma gida jiya, kuma ya gaya masa cewa zai tuntube ni.
Ana haka sai ga wasu manya a unguwa da kuma 'yan siyasa suka zo suka fada masa cewa Yayi yana neman shi, shi kuma ya dauka karya ake yi amsa.
Portable ya tambaye su:
“Ashe ku ne za ku gaya mani cewa Yayi yana nemana? Ina tsammanin suna son damfara ta ne, kamar yadda suka yi a baya lokacin da Yayi ya tura kuɗi. A wancan lokacin ban samu ko sisi ba."
Ya gode wa Allah da miliyoyin da ya samu a sanadiyyar tallata ‘dan takarar gwamnan na APC.

Kara karanta wannan
Bidiyon minista tana raba ɗauri ɗaurin N100,000 ya tada kura, mutane sun dura kanta
Mai tallar APC ya ji kunya a bainar jama'a
An ji labari cewa Alwan Hassan na kwamitin zaben Bola Tinubu ya dage cewa ana iya kiran 112 domin neman agaji gaggawa a kokarin gwamnatin APC.
A dalilin haka kuwa a karshe aka kure shi a tsakiyar shirin talabijin domin da aka kira akwatin wayar, haka nan aka hakura domin kuwa lambar ba ta shiga.
Ba a dade da haka ba sai ga sanarwa daga Femi Gbajabiamila cewa an takaita wadanda za su rika magana da yawun jam'iyyar APC a zaben takarar 2027.
Asali: Legit.ng
