Abubuwa 5 da Ya Kamata Kowa Ya Yi kafin Ranar Zaben 2027

Abubuwa 5 da Ya Kamata Kowa Ya Yi kafin Ranar Zaben 2027

  • Hukumar zabe ta INEC ta sanya ranar 16 ga Janairu, 2027 domin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya
  • A daya bangaren kuma, zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi kuma zai gudana ne a ranar 6 ga Fabrairu, 2027
  • Masu kada kuri'a na bukatar karbar katin PVC, tabbatar da rumfar zabensu, nazarin manufofin 'yan takara da sauransu kafin ranar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Yayin da ake tunkarar babban zaben Najeriya na 2027, masu kada kuri'a na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen zabar shugabannin da za su jagoranci kasar.

Bayan fita kada kuri'a a ranar zabe, akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata masu zabe su tanada tun da wuri domin kada su fuskanci matsaloli.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gargadi 'yan siyasa bayan kai wa Pantami da 'yan NDC hari

Wajen da aka yi a Gombe
Mutane a wajen zaben da aka yi a Gombe a 2026. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa INEC ta sanya ranar 16 ga Janairu, 2027 domin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Abubuwa 5 da ya kamata masu zabe su yi

1. Karbar katin PVC

Abu na farko da ya kamata masu zabe su yi shi ne tabbatar da cewa sun yi rajista a hukumar INEC kuma sun karbi katin zabensu na dindindin (PVC).

Daraktar wayar da kan masu zabe da yada bayanai ta INEC, Victoria Eta-Messi, ta bayyana karbar katin PVC a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata a kammala kafin zabe.

Ta bukaci wadanda suka yi rajista su je su karbi katunansu, tare da karfafa wa makwabtansu gwiwa su yi hakan.

2. Tabbatar da rumfar zabe

Masu zabe su tabbatar da inda rumfar zaben da aka ware musu take tun kafin ranar zabe, maimakon jiran ranar zabe kafin su fara neman inda za su kada kuri'a.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya yi magana kan damar Atiku da Obi a 2027

Wani mamba a kwamitin gudanarwa na kungiyar Yiaga Africa, Farfesa Nnamdi Aduba, ya shawarci masu zabe su san wuraren da za su kada kuri'a tun da wuri.

Ya kuma bukace su da su kasance cikin shiri, su rike wayoyinsu da lambobin jami'an zabe da na tsaro, ciki har da kwamishinan zabe na jihohinsu da 'yan sanda, domin samun saukin tuntuba idan bukatar hakan ta taso.

Shugaban kungiyar Nigerian Society of International Affairs, Farfesa Hassan Saliu, ya kuma bukaci masu zabe su yi la'akari da nisan da ke tsakanin gidajensu da rumfunan zabe, tare da tanadar hanyar zuwa wuraren.

3. Nazarin manufofin 'yan takara

Kafin zabe, ya kamata masu kada kuri'a su karanta tare da fahimtar manufofin jam'iyyun siyasa da alkawuran 'yan takara.

Farfesa Saliu ya ce masu zabe su tantance manufofin kowace jam'iyya, su gano wadanda suka dace da bukatunsu, sannan su duba irin amincewar da suke da ita ga 'yan takarar.

Farfesa Amupitan a ofis
Shugaban INEC, Joash Amupitan a ofis. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ya shawarci masu zabe su tambayi kansu ko alkawuran 'yan takara za su yiwu, yadda za su aiwatar da su da kuma ko tarihin ayyukansu na baya ya tabbatar da ikirarin da suke yi.

Kara karanta wannan

Matakin da yan sanda suka dauka kan farmakin tawagar Pantami a Gombe

4. Tantance labaran siyasa

Lokutan zabe na zuwa da yaduwar labaran karya, bidiyoyin bogi da bayanan da aka kirkira domin bata sunan 'yan takara ko jam'iyyun siyasa.

Aduba ya shawarci masu zabe kada su dauki duk wani sako da suka gani a WhatsApp, Facebook, TikTok ko wasu kafafen sada zumunta a matsayin gaskiya.

Ya ce ya kamata su binciki inda labari ya fito, ranar da aka wallafa shi da kuma cikakken bayanin da ke tattare da shi kafin su yarda da shi ko su yada shi.

Ya kuma bukaci masu zabe su rika tabbatar da bayanai ta kafafen yada labarai masu inganci, sanarwar hukumomi da shafukan tantance sahihancin labarai.

5. Kin amincewa da sayen kuri'a

Masu zabe na bukatar su kasance cikin shiri tare da lura da yanayin tsaro kafin zabe, lokacin kada kuri'a da kuma bayan kammala zaben.

Aduba ya bukaci INEC ta tanadi wani shiri na daban kan yadda za a kai kayayyakin zabe rumfunan kada kuri'a idan aka samu matsala da tsarin sufuri.

Kara karanta wannan

Zamfara: An sanar da sakamakon zaben fitar da gwanin dan majalisar tarayyar APC

A nasa bangaren, Farfesa Saliu ya shawarci masu zabe su ki karbar kudi, abinci, kyaututtuka ko wasu abubuwa daga 'yan siyasa domin musanya da kuri'arsu.

Ya ce bai kamata masu zabe su bari abin da za su samu na dan lokaci ya rinjayi zabinsu ba, maimakon su zabi wanda suke ganin zai iya cika alkawuran da ya dauka.

Ya kuma bukace su da su san hakkokinsu da tsarin kada kuri'a, tare da sanin hanyoyin kai rahoton barazana, sayen kuri'a da sauran magudin zabe ga hukumomin da suka dace.

ADC ta ce Atiku Abubakar zai yi takara

A wani labarin, kun ji cewa sakataren yada labaran jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce jam'iyyarsa za ta shiga zaben 2027 duk da rikicin shugabanci da shari'o'in da take fuskanta.

Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin wata hira a ranar Alhamis, inda ya tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai kasance cikin wadanda za su tsaya takara.

Ya kuma zargi jam'iyyar APC mai mulki da kokarin raunana 'yan adawa ta hanyar shari'o'i, yana mai cewa ADC ta shafe lokaci mai yawa a kotuna maimakon gina rassanta da shirya yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng