Nafiu Bala da David Mark: An Dauko Tsohon Hoto Ana Amfani da Shi a Yada Karya a Fadan ADC
- Kwanan nan wasu suka rika yawo da wata takarda da sunan Nafiu Bala Gombe ya yi murabus daga jam’iyyar ADC
- Bincike ya nuna tsohuwar wasika ce aka dauko, a karshe ma an fahimci ba ta kunshe da sa hannun matashin ‘dan siyasar
- Ban da binciken da Legit Hausa ta yi, kotun tarayya ma ta yanke hukunci cewa kirkirar wannan takardar murabus aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - A cikin makon nan kawai wasu suka rika yawo da jita-jita cewa wai Alhaji Nafiu Bala Gombe ya yi murabus daga cikin jam’iyyar ADC.
Labari ya yi ta yawo musamman a dandalin X da ya fi shahara da Twitter cewa Nafiu Bala Gombe ya rubuta takardar barin jam’iyyar adawar.

Source: Facebook
Rade-radin murabus din Nafiu Bala daga ADC
Nuhu Sada wanda ya nemi kujerar Majalisar dokoki a jihar Kaduna yana cikin wadanda aka fara ganin hoton a shafinsa a X a ranar Laraba.
Ya wallafa cewa:
LABARI DA DUMI-DUMI: NAFIU BALA NA GOMBE YA YI MURABUS DAGA APC.
Ga sanarwar murabus din shi nan, ana zargin INEC ta karba kuma ta buga hadimi. Murabus din Nafiu Bala ta kawo karshen Bola Tinubu da APC.
Barka ga Mai girma David Mark da Alhaji Atiku Abubakar.
Da gaske Nafiu Bala ya bar ADC?
Legit Hausa ta binciki wannan hoto kuma ta tabbatar da cewa takardar ta yi kama da ta murabus da Nafiu Bala ya rubuta don ya bar ADC.
Amma da aka laluba da kyau, sai aka ga duk cewa takardar ta yi kama da ta gaskiya, babu abin da zai nuna ba daga wajen Nafiu Bala ta fito ba.
Inda gizo yake sakar shi ne, tsohon hoto ne aka sake kakkabe shi a matsayin wani sabon lamari.
Duk wanda ya lura da takardar da kyau, zai ga cewa yana dauke da kwanan watan Agustan 2025, yau fiye da shekara kenan da fitowar takardar.

Kara karanta wannan
Da gaske shugaban INEC ya yi amfani da shafinsa na X wajen tallata Tinubu? Gaskiya ta bayyana
Takardar tana dauke da hatimin hukumar zabe na kasa wato INEC a ranar 10 ga watan Oktoba 2025.
Tun 2025 Nafiu Bala ya karyata labarin
Kuma ko da aka bincika da kyau a yanar gizo, fasahar Reverse Image na Google ya nuna wannan wasika ta fi watanni bakwai tana yawo a duniya.
Rahotanni daga jaridu da dama sun ce tsohon mataimakin shugaban ADC ya nesanta kan shi da takardar, ya ce sam ba sa-hannun sa ba ne a kai.
A wata hira da Arise, Bala Sani wanda shi ne shugaban ma’aikatan Nafiu, ya tabbatar da batun, ya ce mai gidansa bai hakura da matsayinsa a ADC ba.
Kotu ta kawo karshen rikicin sahihancin takardar murabus
Ko da ba a yarda da shi ba, uwa-uba, sai kotu ta yi hukuncin da dole ya raba gardama a rikicin.
A karshe dai da aka je wani kotun tarayya mai zama a birnin Abuja, alkali ya yanke hukunci cewa wannan wasikar murabus ba ta gaskiya ba ce.
Lauyoyin David Mark sun yi kokarin nuna wa Mai shari’a Peter Lifu cewa matashin ya bar jam’iyyar ADC tun ranar 25 ga watan Satumba 2025.

Kara karanta wannan
Kaduna: Yara da magoya bayan El Rufai sun yi watsi da ADC, sun koma jam’iyyar APC
Daga nan kuma suka ce ya rubuta wasika yana sanar da cewa ya bar jam’iyyar ADC wanda a baya shi ne shugaban nata a yankin Arewa maso gabas.
Don haka wannan labari irin wanda ake dauko tsohon bayani ne a wanke shi, sai a sake yada wa kuma wani ne ya sa hannu da sunan Nafiu Bala.
'Yan ADC sun tsallaka APC a Kaduna
An ji labari wasu masu biyayya ga Nasir El-Rufai sun koma APC a Kaduna, sun ce sun gaza gane kan ‘dan takaran jam’iyyar ADC, Isa Ashiru Kudan.
Matasan sun koma jam'iyyar APC ne domin nuna cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Gwamna Uba Sani, suna ganin ya cancanci a yaba masa.
Masu sauya shekar sun hada da kungiyoyin matasa, tsofaffin ƴan takara da shugabannin jam'iyyar ADC na kananan hukumomi a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng
