Kwana Ya Kare: Jarumin Fim da ke Fama da Rashin Lafiya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Jarumin Fim da ke Fama da Rashin Lafiya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood da ke Kudancin Najeriya, Diewait Ikpechukwu, ya rasu yana da shekara 71
  • Jarumin, wanda tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ya rasu ne ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, 2026 bayan fama da doguwar jinya
  • Wata majiya daga iyalansa ce ta tabbatar da rasuwarsa amma har yanzu ba a samu cikakkun bayanai kan rasuwarsa da shirye-shiryen jana'iza ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rahotanni sun nuna cewa fitaccen jarumin fina-finai a masana'antar Nollywood da ke Kudancin Najeriya, Diewait Ikpechukwu, ya rasu yana da shekara 71 a duniya.

An ruwaito cewa Ikpechukwu, wanda tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne, ya rasu ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, 2026.

Jarumin Nollywood, Diewait Ikpechukwu.
Jarumin masana'antar Nollywood da ke Kudancin Najeriya, Diewait Ikpechukwu Hoto: Ebube Obi
Source: Facebook

Wata majiya daga iyalansa ta bayyana wa jaridar Vanguard cewa jarumin ya riga mu gidan gaskiya ne bayan fama da doguwar jinya, ya mutu yana da shekaru 71 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Moniepoint ya fitar da hanya mai sauki ta duba waɗanda za su samu tallafin N50,000

Sai dai har zuwa okacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakkun bayanai kan musabbabin rasuwarsa ba da juma shirye-shiryen jana'iza ba.

Rasuwarsa ta ƙara zama wani babban rashi ga masana’antar shirya fina-finai ta Najeriya.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262