
Dandalin Kannywood







Hadiza Gabon ta ce 'yan mata su daina damuwa da saurayinsu kawai, su auri mijin da ya dace, ko da mijin wata ne, a cewar wani sako daga Hassan Giggs.

Shekarar ta 2025 za ta zamo shekarar da za a ga sababbin finafinan Hausa da salon daukarsu ya sha bamban da na baya. Mun zakulo finafinai 6 da za a haska a 2025.

Jaruma Radeeya Jibril ta yi aure, ta gode wa wasu 'yan masana'antar finafinan, tana mai alfahari da Kannywood, kuma ta nemi yafiya ga duk wanda ta yiwa ba daidai ba.

Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta dakatar da jarumar Kannywood Samha M Inuwa saboda yaɗa bidiyoyi da hotunan da ba su dace ba a kafafen sadarwa.

Matar mawaki Ado Gwanja, Maryam, ta haifi ɗa namiji mai suna Nawab. Mutane sun taya su murna tare da addu’ar Allah ya raya yaran cikin Musulunci.

An samu ci gaba sosai a harkar finafinan Hausa a shekarar 2024 da ta gabata. Legit Hausa ta zakulo wasu finafinai 5 da suka yi tashe a shekarar da ta gabata.

Allah ya yiwa mahaifiyar marigayi Ahmad S Nuhu rasuwa. Shugaban hukumar fina finan Najeriya, Ali Nuhu ya sanar da lokacin da za a yi mata jana'iza a Jos.

Mawaka irinsu Sadiq Saleh, Ado Gwanja, da Umar M Shareef sun yi fice a 2024 da wakokinsu na soyayya, al'adun Hausa, da kuma salon da ke sanya rawa a gidajen biki.

Ali Nuhu ya gargadi jaruma Rayya kan yunkurin da take yi na zana tattoo. 'Yan Kannywood da dama sun mara masa baya, suna neman ta dakatar da wannan shiri.
Dandalin Kannywood
Samu kari