Dandalin Kannywood: Auren wata jarumar fim din hausa ya mutu a kasa da wata 3

Dandalin Kannywood: Auren wata jarumar fim din hausa ya mutu a kasa da wata 3

- Auren wata jarumar fim din hausa ya mutu a kasa da wata 3

- Mijin Jaruma Sadiya Kabala ya fallasa dalilin da yasa ya sakin ta

- Yace maza take kawo masa gidan sa

Yayin da jaruman fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ke cigaba da fuskantar suka daga al'ummar Hausawa musamman ma akan rashin zaman aure, auren wata jarumar mai suna Sadiya Kabala ya sake mutuwa.

Dandalin Kannywood: Auren wata jarumar fim din hausa ya mutu a kasa da wata 3
Dandalin Kannywood: Auren wata jarumar fim din hausa ya mutu a kasa da wata 3
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jerin kasashe 10 mafi karancin mutane a duniya

Sai dai ita lamarin nata ya sha banbab domin kuwa ya dauki hankalin al'umma musamman ma masu sha'awar harkokin fina-finan Hausar da dama bisa la'akari da cewa auren kwata-kwata bai cika watannin uku da yi ba.

Legit.ng ta samu cewa mijin nata, Honorabul Ahmed Isah wanda ya yi fira da majiyar mu ta mujallar Fim ya fadi dalilin da yasa ya saki matar tasa inda yace tana kawo masa katti ne a cikin gidan sa na aure.

Honorabul Ahmad ya kara da cewa a lokuta da dama ya sha samun kato a cikin gidan sa kuma duk da irin nasihar da yayi mata, tsohuwar matar ta sa taki ta gyara halin ta wanda hakan ya tunzura shi har ta kai ga ya sake ta.

A watan Aprilu ne dai jarumar ta angwance tare da angonta Honourable Ahmad Isah, a wani bikin da ba wani abokin sana'arta da aka gani yaje wajen daurin auren hatta maigidanta a harkar fim wato Adam A Zango.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel