Tinubu Ya Leƙo Babbar Matsalar Ƴan Plateau, Ya Ɗauka Masu Alƙawari
- Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen girka kyamarorin sa ido a Filato
- Gwamnatin tarayya ta dauki jami'an tsaron gandun daji 1,000 aiki, inda a halin yanzu suke karbar horon da zai ba su damar fara gudanar da ayyukansu
- Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana shirin samar da guraben ayyukan yi ga matasa 2,000 ta hanyar hada su da kamfanoni da kungiyoyin kasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau –Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wasu daga cikin matakan da gwamnatinsa ke dauka domin dakile matsalar tsaro.
Bola Tinubu ya bukaci mazauna jihar su ci gaba da mara wa APC baya har zuwa babban zaben 2027.

Source: Facebook
Tiinubu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da jam'iyyar APC ta gudanar da taron yakin neman zabenta a filin wasa na Zaria Road da ke Jos, wanda aka kiyasta yana da damar daukar mutum 60,000, cewar Channes TV.
A jawabinsa, Tinubu ya kuma jaddada bukatar hadin kan 'yan kasa, yana mai cewa addini, kabila ko al'adar mutum bai kamata su zama dalilin rarrabuwar kawuna tsakanin al'ummar Najeriya ba.
Savabbin matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka kan tsaro
Da yake magana kan matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu sassan Filato, shugaban kasar ya sanar da cewa kayan aikin kyamarorin sa ido da ya yi alkawarin samarwa jihar sun shigo Najeriya.
Ya ce nan ba da dadewa ba za a fara girka na'urorin, domin su taimaka wa hukumomin tsaro wajen bibiyar abubuwan da ke faruwa da kuma gano wadanda ke da hannu wajen aikata laifuka.
Tinubu ya kuma bayyana cewa jami'an gandun daji 1,000 da gwamnatin tarayya ta dauka aiki suna gudanar da atisayen horaswa, cewar Punch.
A cewarsa, za su fara gudanar da ayyukansu bayan kammala shirin horaswar, musamman wajen sa ido a dazuzzuka da sauran wuraren da ake zargin masu aikata laifuka na amfani da su.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa kafa rundunar 'yan sandan jihohi na daya daga cikin shirye-shiryen da ake sa ran za su taimaka wajen inganta harkokin tsaro a Najeriya.

Source: Facebook
Mutfwang ya shirya daukar matasa 2,000 aiki
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin tarayya bisa tallafin da jihar ke samu wajen aiwatar da ayyukan more rayuwa a bangarorin sufuri, ilimi da kiwon lafiya.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa na kokarin bude wata hanya ta samun aikin yi ga matasa kusan 2,000 ta hanyar kulla alaka da kamfanoni da kungiyoyi da ke Amurka da Turai.
A cewarsa, tsarin zai bai wa matasan damar samun ayyukan da za su rika gudanarwa ta yanar gizo, ba tare da bukatar tafiya kasashen da kamfanonin suke ba.
Tinubu ya gargadi yan siyasa
Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da karuwar tashe-tashen hankula a harkokin siyasa a sassan Najeriya.
Tinubu ya gargadi 'yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani hali na rashin da'a yayin da ake tunkarar zaben 2027.
A bayanin da ya yi, shugaban kasar ya ce ba za a lamunci duk wani rashin da'a daga 'yan siyasa da magoya bayansu ba.
Asali: Legit.ng

