Kannywood: Akwai dadi; Ladidi 'Tubeless' ta yi kira ga maza su rika auren 'yan fim

Kannywood: Akwai dadi; Ladidi 'Tubeless' ta yi kira ga maza su rika auren 'yan fim

Daya daga cikin fitattun jaruman nan na masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood mai fitowa a matsayin uwa wadda Ladidi Abdullahi amma wadda aka fi sani da Ladidi Tube less ta yi ikirarin cewa duk duniya babbu mace mai dadin aure kamar 'yar fim.

Ladidi ta kara da cewa ita 'yar fim saboda irin yadda take taka rawa a cikin fina-finai, tana kara ilimin zamantakewa irin ta aure sosai a don haka ne ma take kira ga maza su rika auren 'yan fim din.

Kannywood: Akwai dadi; Ladidi 'Tubeless' ta yi kira ga maza su rika auren 'yan fim
Kannywood: Akwai dadi; Ladidi 'Tubeless' ta yi kira ga maza su rika auren 'yan fim
Asali: Facebook

Hajiya Ladidi kamar dai yadda muka samu ta yi wannan ikirarin ne a yayin wata fira da ta gudanar da wakilin majiyar mu a garin Kaduna dake zaman mahaifar ta.

Legit.ng ta samu cewa jarumar ta bayyana cewa abun takaici ne yadda mutane ke yi wa 'yan matan fim din mummunar fahimta musamman ma yadda su ke gudun auren su alhali kuma sun fi kowa dadin aure.

Haka ma dai jarumar da aka bukaci ta bayar da shawara zuwa ga sauran matan da ke harkar fim din sai ta ce "Shawara ta gare su shi ne su yi karatu, saboda na ga gaba abubuwa za su canje wanda zai kai lokaci da sai kana da karatu za ka yi shi kansa fim din ma."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng