"Shugaba Tinubu ba Zai Lamunci a Taba Mutuncin Marigayi Buhari a Gabansa ba"

"Shugaba Tinubu ba Zai Lamunci a Taba Mutuncin Marigayi Buhari a Gabansa ba"

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce Bola Tinubu ba zai lamunci duk wanda ya raina ko ya soki marigayi Muhammadu Buhari a gabansa ba
  • Shettima ya ce Tinubu na matukar girmama tsohon shugaban kasar, duk da cewa ya karbi ragamar mulki tare da kalubalen da ya gada
  • Ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai kawo sauyi, yana mai cewa ajiyar kudaden waje ta Najeriya na kusa da dala biliyan 60

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, Nigeria - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai lamunci duk wanda ya raina ko ya taba mutuncin marigayi Muhammadu Buhari a gabansa ba.

Shettima ya bayyana cewa Tinubu na matukar girmama wanda ya gada a kan mulki watau tsohon shugaban kasa, Muhammdu Buhari, wanda Allah Ya yi wa rasuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a wurin kamfen APC a Plateau Hoto: Stanley Okwocha
Source: Facebook

Leadership ta ruwaito cewa Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a jihar Filato.

Shettima ya kare salon mulkin Tinubu

Sanata Kashim Shettima ya kare salon mulkin Tinubu da kuma matakin da ya dauka na karbar alhakin kalubalen da kasar ke fuskanta maimakon dora laifi kan gwamnatin da ta gabata.

Maganganun mataimakin shugaban kasar sun zo ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin da tsohon Ministan Sufuri kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya yi wa Buhari.

Amaechi ya zargi marigayi shugaban kasar da yaudararsa kan wani alkawarin da ya ce ya yi masa na mara wa burinsa na zama shugaban kasa baya da kuma tabbatar masa da tikitin takarar APC gabanin zaben 2023.

A baya Shettima ya mayar da martani kan zarge-zargen Amaechi a jihar Jigawa, inda ya kare marigayi shugaban kasar da tarihin siyasarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan yan Najeriya kan yadda za a gudanar da zaben 2027

"Tinubu ba zai bari a taba Buhari ba"

Da yake jawabi a gangamin na Filato, Shettima ya ce shugabanni da dama idan sun hau mulki, sukan zargi wadanda suka gabace su ko kuma su guji daukar alhakin matsalolin da suka gada.

Sai dai ya ce Tinubu ya zabi wata hanya ta daban, inda ya amince ya karbi kadarori da kuma basussuka da nauyin da gwamnatin da ta gabata ta bari.

Shettima ya ce:

“Shugabanni da dama idan sun karbi ragamar mulki, suna da zabi biyu: ko dai su ci gaba da tura matsala zuwa gaba ko kuma su dora laifi kan wadanda suka gabace su.
“Amma Shugaba Tinubu, lokacin da ya karbi ragamar mulki, a cewarsa, dole ne ya karbi kadarori da kuma basussuka da nauyin wanda ya gabace shi.
“Kuma komai girman girmamawar da yake yi maka, ba zai bari ka taba marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a gabansa ba."
Tinubu da Buhari.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da marigayi Muhammadu Buhari Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai kawo sauyi, wanda ya dauki matakai masu wahala domin hana tattalin arzikin Najeriya durkushewa lokacin da ya hau mulki a watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

'Na yi mamakin abin da Atiku ya yi mini': Nafiu Bala ya yi ɓarin zance

Yan Najeriya sun fara kewar Buhari

Kun ji cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya ce ’yan Najeriya sun fara kewar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Amaechi ya bayyana cewa, a ra’ayinsa, rayuwa ta fi sauƙi a lokacin mulkin marigayi Buhari fiye da yadda take a ƙarƙashin gwamnatin APC mai ci yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262