Dandalin Kannywood: Auren 'yan fim 6 ya mutu a wannan shekarar

Dandalin Kannywood: Auren 'yan fim 6 ya mutu a wannan shekarar

Rahotannin da muke samu daga majiyar mu ta Fim mai wallafa mujallar da ta shafi harkokin fina-finan Hausau ta bayyana cewa kimanin akalla auren mata 'yan fim shidda ne ya mutu a shekarar nan da muke ciki ta 2017.

Haka ma dai mujallar ta bayyana hakan tamkar wani babban bala'i ko kuma annoba da ta fadawa 'yan masana'antar kasantuwar ba'a taba samun mace-macen aure da yawan da suka kai haka ba a cikin shekara daya.

Dandalin Kannywood: Auren 'yan fim 6 ya mutu a wannan shekarar
Dandalin Kannywood: Auren 'yan fim 6 ya mutu a wannan shekarar

KU KARANTA: Ronaldo ne yafi kowa iya kwallo a duniya

Legit.ng dai har ila yau ta samu cewa ganin haka ne ma ya sanya majiyar tamu ta shiga yin bincike don sanin ainahin musabbabin mutuwar auren na jaruman masana'antar.

Wasu daga cikin matan dai sun bayyana cewa laifin mazan ne domin kuwa sun sa yaudara wajen neman auren nasu yayin da wasu kuma daga cikin matan suka bayyana cewa mazajen nasu ba su basu abinci.

Da majiyar tamu ta tuntubi wasu mazan da lamarin ya shafa daya daga cikin su ya bayyana cewa ita wadda ya auran tace wai bata son kishiya ne shi kuma ya ga kamata su rabu da ita.

Matan dai da auren nasu ya mutun sun hada da Fauziyya Maikyau, Maryam Isah, Fati Al-Amin, Aisha Tafida, Safiya Kishiya da kuma Asma'u Musa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng