Dalibar Jami'a a Najeriya Ta Yi Garkuwa da Kanta, Ta Kwana a Dakin Saurayinta
- 'Yan sandan Ekiti sun kama wata dalibar jami'a, Helen Kayode bisa zargin yin garkuwa da kanta don kawai ta debe wa saurayinta kewa
- Dalibar ta aika wa 'yar uwarta saƙon ƙarya cewa an yi garkuwa da ita, amma bincike ya nuna ta kwana tare da saurayinta a Ado-Ekiti
- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi Allah wadai da abin da dalibar ta aikata, inda ya ce za a gurfanar da ita gaban kotu da an gama bincike
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - A wani yanayi na ban mamaki, rundunar 'yan sandan jihar Ekiti ta kama wata dalibar ajin ƙarshe a jami'ar jihar Ekiti (EKSU), Helen Kayode.
An ce, abin da ya bai wa mutane mamaki shi ne yadda aka kama dalibar bisa zargin shirya garkuwa da kanta don kawai ta debe wa saurayinta kewa.

Asali: Twitter
An cafke dalibar da ta yi garkuwa da kanta
'Yan sandan sun sanar da kama Helen Kayode a ranar Alhamis, inda suka ce aikin nata ya haifar da firgici a yankin Iworoko-Ekiti da Ado-Ekiti, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton 'yan sandan ya nuna cewa dalibai ta aika wani saƙo ga 'yar uwarta a ranar 1 ga Mayu, inda ta yi ikirarin cewa ta shiga wata mota, kuma an yi garkuwa da ita.
A cewar mai magana da yawun rundunar, SP Sunday Abutu, saƙon dalibar da ya yadu ya haifar da firgici a tsakanin jama'a kuma ya dagula zaman lafiya da tsaron da ake samu a jihar.
Dalibar ta boye ne a dakin saurayinta
SP Sunday ya bayyana cewa Helen ta ce an yi garkuwa da ita tare da ajiye ta a wani gini da ba a kammala ba wanda ta ce yake kewaye da kurmi.
Kakakin rundunar ya nuna damuwa cewa bayanin ya yadu a kafafen sada zumunta, wanda ya haifar da wasu martani da suka kawo cikas ga tsaro da zaman lafiya.
Binciken da 'yan sanda suka yi ya nuna cewa ba a yi garkuwa da dalibar ba, hasalima, ta kwana ne a dakin saurayinta kafin ta tafi Legas.
SP Sunday ya ce:
"Wacce ake zargin ta amsa laifinta, ta shaida mana cewa ta yi ƙaryar ne don ta samu damar halartar bikin zagayowar ranar haihuwarta tare da saurayinta a Ado-Ekiti, saboda ya yi mata alƙawarin 'kyauta ta musamman'."

Asali: Twitter
Za a gurfanar da dalibar a gaban kotu
Jaridar The Nation ta ruwaito jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda ya kara da cewa:
"Dalibar ta ce iyayenta sun matsa mata a kan ta koma Legas ba tare da son ranta ba, wannan ne ya sa ta yanke shawarar yin garkuwa da kanta don zama da saurayinta."
Kwamishinan 'yan sandan jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya yi Allah wadai da lamarin, yana mai gargadin cewa duk wanda ya yada ƙarya zai fuskanci fushin doka.
Joseph Eribo ya ce za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike kuma ya sake tabbatar da ƙudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
An kama budurwar da ta yi garkuwa da kanta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, a jihar Akwa Ibom, rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata da ta shirya garkuwa da kanta tare da hadin bakin saurayinta.
Matar ta amsa laifinta bayan 'yan sanda sun kama ta, inda ta ce ta hada kai da saurayinta da wasu mutane uku don su karɓi kuɗi daga yayarta da ke ƙasar waje.
Bugu da ƙari, 'yan sanda sun kama mutane 52 bisa zargin aikata laifuffukan da suka haɗa da kisa, garkuwa da mutane, fashi da makami, shiga ƙungiyar asiri, da sauransu.
Asali: Legit.ng