"Yadda Aka Dakatar da Limamin Masallaci saboda Ya Ja Atiku Abubakar Sallah"
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi wasu ’yan siyasa da tsangwamar mutanen da ke mu’amala da shi
- Atiku, dan takarar shugaban kasa na APM, ya yi zargin cewa an dakatar da wani limami bayan ya jagoranci sallar jam’i da ya halarta
- Dan takarar shugaban kasar na ADC ya yi wannan magana ne yayin ziyarar ban girma da ya kai fadar Sarkin Bauchi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi wasu ’yan siyasa, musamma gwamnoni, da tsangwamar mutanen da ke tare da shi.
Atiku ya yi zargin cewa an dakatar da wani limami daga aikinsa na limanci bayan ya jagoranci sallar jam’in da ya halarta.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, a yayin ci gaba da yakin neman zabensa.
Atiku Abubakar ya ce ya kai ziyara fadar ne domin girmamawa da nuna mutunci ga masarautun gargajiya.
“Mai martaba, a wurina nan ne gida na. Na zo fadar ne domin girmama mahaifinmu na da kuma gaishe shi.”
Atiku ya tambayi dalilin da ya sa ’yan siyasa da dama ke komawa masarautun gargajiya domin karbar sarauta bayan sun bar mukamansu na gwamnati.
“Ina son in yi tambaya: Me ya sa ’yan siyasa ke komawa masarautunsu domin neman sarauta bayan sun bar mukaman gwamnati? Ko kai shugaban kasa ne, gwamna, sanata ko minista, da zarar wa’adinka ya kare, sai ka koma fada domin karbar sarautar gargajiya, saboda wannan ne tushenmu kuma makomarmu.
“Muna matukar godiya da wannan dama da aka ba mu ta ziyartar mai martaba da kuma girmama shi a Bauchi,” in ji shi.
Atiku ya yabawa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, bisa ba shi damar ziyartar masarautun gargajiya na jihar ba tare da wani shamaki ba.
“Ina son in mika godiya ta musamman ga Gwamnan Jihar Bauchi saboda kyakkyawar tarbar da ya yi mana. Domin a wurare da dama da muke ziyarta, ba sa barin mu gana da sarakunan gargajiya.
“Wannan mummunar dabi’a ta kai matsayin da aka dakatar da wani limami a masallacin da na yi sallah.
"Wannan ne ya sa na yi tambaya: A tarihin Arewacin Najeriya, na san cewa limami yana karkashin ikon sarki ne ba gwamna ba. Domin gwamna zai kammala wa’adinsa ya bar ofis, amma sarki zai ci gaba da zama a kan sarautarsa.
Atiku ya tausaya wa yan Najeriya
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna tausayawarsa ga ’yan Najeriya kan halin kuncin da suke ciki.
Ya duba matsin tattalin arzikin da suke fuskanta sakamakon tsadar kayayyaki da sauran manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Atiku ya yi kira ga gwamnatin Tinubu ta magance tsadar makamashi da rashin samun lamuni mai sauƙi domin farfaɗo da masana’antun cikin gida.
Asali: Legit.ng

