Mafa: Wani Bam Ya Tashi da Mutane a Hanyar zuwa Filin Sabon Masallacin Juma'a

Mafa: Wani Bam Ya Tashi da Mutane a Hanyar zuwa Filin Sabon Masallacin Juma'a

  • Wani bam da aka dasa a ƙarƙashin ƙasa ya tashi da ƙananan yara a hanyar zuwa filin da ake gina sabon masallacin Juma'a a Mafa ta jihar Borno
  • Rahotanni sun nuna cewa yaran sun tono bam ɗin ba tare da sani ba kuma ya tashi da su a ranar Alhamis, 8 ga watan Mayu, 2025
  • Yara biyar sun jikkata, ɗaya daga cikinsu ya rasu hannu guda kuma yanzu haka an garzaya da su asibiti domin ba su kulawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Wani bam da ake kyautata zaton ƴan ta'adda ne suka dasa shi a ƙarƙashin ƙasa ya fashe a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a Arewa maso Gabas.

An ruwaito cewa fashewar bam ɗin, wanda ya faru jiya Alhamis, 8 ga watan Mayu, 2025 ya jikkata yara biyar, ɗaya daga cikinsu ya rasa hannunsa.

Jihar Borno.
Bam ya tashi da kananan yara a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na X yau Juma'a, 9 ga Mayu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bam ya tashi da ƙananan yara a Borno

Ya ce rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 2:25 na rana, lokacin da yaran suka kama wasa da bam din ba tare da sani ba.

A cewarsa, bayanai sun nuna an birne bam din ne a cikin ramuka kusa da wata gada da ke hanyar zuwa wurin aikin gina sabon masallacin Juma'a na Mafa.

Yaran da abin ya rutsa da su sun hada da Abdullahi Umar, Musa Mele, Fatima Abacha, Abba Kawu Muhammed da Khalid Alhaji Bukar.

Makama ya ce dukkansu mazauna garin Mafa ne kuma sun samu raunuka daban-daban, ciki har da daya da ya rasa hannusa guda.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Bayan faruwar lamarin, kwararru daga sashen kwance bam watau EOD-CBRN, 'yan sanda daga ofishin Mafa, da 'yan banga na CJTF sun kai ɗauki wajen.

An ce dakarun tsaron sun rufe wurin, inda suka fara bincike don gano sauran bama-baman da wataƙila aka birne.

An tabbatar da cewa sun kuma gano wasu bangarorin kwano da aka sarrafa su a matsayin bam, inda suka lalata su cikin kwarewa.

"Yara hudu daga cikin wadanda suka jikkata an garzaya da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) don samun kulawar likitocin
"Ragowar ɗayan wanda raunin da ya samu kaɗan ne an kwantar da shi a Asibitin Mafa, inda daga bisani aka sallame shi," in ji Zagazola Makama.

Don kare faruwar irin haka, jami'an EOD-CBRN sun yi ƙoƙarin wayar da kan jama’a da yara kan yadda za su kare kansu daga hadurran ababen fashewa a yankin Mafa.

Ƴan Boko Haram sun kashe kyaftin a Borno

A wani rahoton, mun kawo maku cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun kashe sojan da ya kai muƙamin kyaftin a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa sojan ya rasa rayuwarsa ne yayin da ƴan ta'addan suka kai farmaki ƙauyen Izge da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba da ta gabata da misalin karfe 1:00 na dare, inda suka kuma kashe ƙarin soja guda ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262