'Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannu da Suka Fafata da 'Yan Sanda a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannu da Suka Fafata da 'Yan Sanda a Sokoto

  • 'Yan sandan Sokoto sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai a kauyen Anada da ke karamar hukumar Binji
  • Jami'an tsaro sun yi musayar wuta da maharan, lamarin da ya sa suka gudu suka bar tumaki 43 da suka sace
  • Babu wani jami'in tsaro ko dan gari da ya rasa rai ko ya ji rauni a yayin harin da 'yan bindigan suka kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Jihar Sokoto - Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Sokoto sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Sokoto.

Jami'an 'yan sandan sun kuma ceto tumaki 43 da 'yan bindiga suka sace daga kauyen Anada da ke karamar hukumar Binji.

'Yan bindiga sun sha kashi a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufa'i, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 31 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda da babban jami'in rundunar sun mutu a Najeriya

Ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare ranar Alhamis, 30 ga watan Yulin 2026 lokacin da 'yan bindiga suka kutsa cikin kauyen da ke wani yanki mai nisa.

Yadda 'yan bindiga suka kai hari

Ahmad Rufa'i ya ce maharan sun rika harbe-harbe ba tare da tsari ba kafin su kwashe tumakin daga kauyen.

Ya ce da samun rahoton harin, shugaban 'yan sanda na shiyyar Binji (DPO) ya gaggauta tura jami'an tsaro zuwa yankin.

Jami'an da aka tura sun hada da tawagar yaki da garkuwa da mutane da kuma rundunar Viable Crimes Response Unit (VCRU).

A cewarsa, jami'an tsaron sun rufe dukkan hanyoyin fita daga kauyen domin hana maharan tserewa.

An kwato tumaki 43 daga hannun 'yan bindiga

Rufa'i ya ce jami'an tsaro sun yi musayar wuta da 'yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu barin tumakin da suka sace tare da tserewa zuwa wani daji da ke kusa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun magantu, sun tsuga miliyoyi na fansar alkalin babbar kotun Kebbi

Sanarwar ta ce:

"An yi nasarar ceto tumaki 43 da aka sace, yayin da babu wani jami'in tsaro ko dan gari da ya rasa rai ko ya ji rauni."

Kakakin rundunar ya kara da cewa jami'an tsaro na ci gaba da sintiri da sa ido a yankin domin gano inda wadanda suka tsere suke tare da kama su.

Kwamishinan 'yan sanda ya yaba

Kwamishinan 'yan sandan jihar Sokoto, Hayatu Hassan Shaffa, ya yaba wa shugaban 'yan sanda na shiyyar Binji da tawagarsa bisa gaggawar da suka yi wajen dakile harin.

Shaffa ya kuma jinjinawa jami'an bisa kwarewa da jajircewar da suka nuna yayin aikin.

Ya bukaci mazauna yankin su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin taimaka wa kokarin yaki da ayyukan ta'addanci.

Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a Sokoto
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi sanadiyyar hallaka a akalla mutum bakwai yayin wani hari da suka kai hari a jihar Sokoto

Hatsabiban 'yan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Tsamaye da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com