Iran Ta Yi Magana, da Yiwuwar Yaki ya Kuma Barkewa tsakanin Kasar Musulunci da Amurka
- Iran ta bayyana cewa akwai yiwuwar kasar ta ci gaba da yaki da Amurka duba da yadda har yanzu aka gaza samun daidaito
- Wani babban jami'i a rundunar sojojin Iran ya ce yunkurin kulla yarjejeniyar zaman lafiya na tangal-tangal, kuma mai yiwuwa yaki ya dawo
- Wannan kalamai na zuwa ne bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya ve bai gamsu da sabon tayin da Iran ta gabatar ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tehran, Iran – Wani babban jami’in soja a Iran ya bayyana cewa akwai yiwuwar sake barkewar fada tsakanin Jamhuriyar Musulunci da Amurka.
Jami'in sojan ya yi wannan furuci ne sa’o’i kadan bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce bai gamsu da sabon kudirin tattaunawa da Iran ta gabatar ba.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa Iran ta mika wannan tayi ga Pakistan a matsayin mai shiga tsakani a daren ranar Alhamis, ba tare da bayyana cikakken abin da ya kunsa ba.
Yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran a karshen watan Fabrairu, 2026 ya tsaya tun ranar 8 ga Afrilu, 2026 sakamakon cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Trump ya yi fatali da tayin Iran
Bayan haka, an yi zagaye daya na tattaunawar sulhu tsakanin wakilan Amurka da na Iran a birnin Islamabad na kasar Pakistan, amma aka tashi ba tare da cimma matsaya ba.
Da yake magana da manema labarai, Trump ya ce:
"A wannan lokaci ban gamsu da abin da suka gabatar mana ba,” yana mai dora laifin tsaikon tattaunawa kan sabanin da ke cikin shugabancin Iran.
Shugaba Trump ya kara da cewa zabi biyu ya rage wa Amurka, ko ta ci gaba da kai farmaki ko kuma a ci gaba da tattaunawa, amma ya fi son hanyar sulhu saboda dalilan jin kai.
Amurka na iya ci gaba da yakin Iran
A ranar Asabar da safe, wani babban jami’i a rundunar tsakiya ta sojin Iran, Mohammad Jafar Asadi, ya ce har yanzu akwai yiwuwar sake barkewar yaki tsakanin kasashen biyu.
“Alamu sun nuna cewa Amurka ba ta da niyyar cika duk wasu alkawurra ko yarjejeniyoyi,'' in ji shi.

Kara karanta wannan
Iran ta karyata Amurka kan asarar da Trump ya yi a yaƙin Isra'ila, ta fadi adadin dalolin
Babban alkalin Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya ce kasarsa ba ta taba kauce wa tattaunawa ba, amma ba za ta amince da sharuddan da ake kokarin tilasta mata ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Twitter
Fadar White House ta ki bayyana cikakkun bayanai kan sabon tayin Iran, amma rahotanni sun nuna cewa tana son a mayar da batun shirin nukiliyar Iran cikin tattaunawa.
Rahotanni sun nuna cewa labarin sabon tayin Iran ya sa farashin mai ya sauka na dan lokaci, amma har yanzu yana sama da yadda yake kafin yakin, sakamakon rufe mashigar Hormuz.
Iran ta mika sabon tayi ga Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Iran ta mika sabon tayi da tsarin tattaunawa ga Amurka ta hannun kasar da ke shiga tsakani watau Pakistan.
Rahotannin da ke shigowa sun ce an mika takardar da ke kunshe da sabon tayin Iran ne a daren ranar Alhamis, amma ba a bayyana cikakken abin da ta kunsa ba.
Wani masani, Farfesa Sultan Barakat, ya ce akwai yiwuwar Amurka ta mayar da hankali kan sabon tayin na Iran, ko da kuwa bai mayar da hankali kai tsaye kan shirin nukiliya ba.
Asali: Legit.ng
