Dattawan Kiristoci Sun Yi Matsaya kan Tazarcen Tinubu a Zaben 2027

Dattawan Kiristoci Sun Yi Matsaya kan Tazarcen Tinubu a Zaben 2027

  • Kungiyar dattawan Kiristoci ta kasa ta ce gwamnatin Bola Tinubu ta gaza a bangaren tsaro, tattalin arziki da walwalar jama'a
  • Dattawan sun bukaci shugaban kasar ya hakura da neman wa'adi na biyu, ya mayar da hankali kan sake fasalin Najeriya
  • Kungiyar ta kuma yi kira ga INEC da bangaren shari'a su tabbatar da gudanar da sahihin zabe cikin adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

FCT, Abuja - Kungiyar Dattawan Kiristoci na Kasa (NCEF) ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya hakura da neman sake tsayawa takara a zaben 2027.

Kungiyar ta ce yadda gwamnatin Tinubu ta gudanar da mulki ya kasance abin takaici kwarai, musamman a bangaren tsaron kasa, bunkasa tattalin arziki da walwalar 'yan Najeriya.

Kiristoci sun bukaci Tinubu ya hakura da takara
Mai girma Bola Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan ranar 9 ga Yulin 2026, wadda shugaban NCEF na kasa, Samuel Gani, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Gobara: 'Yan kasuwar Kano sun bi sawun N5bn na tallafin Tinubu

A cikin sanarwar, dattawan sun ce aikin gwamnatin tarayya bai kai matsayin da ake bukata ba.

NCEF ta bukaci Tinubu ya hakura

Kungiyar ta ce alkiblar da gwamnatin Tinubu ke kai Najeriya tana kara jefa 'yan kasa cikin fargaba maimakon ba su kwarin gwiwa.

A cewar sanarwar:

"Halin da ake ciki ya bar masu kishin kasa ba tare da wani zabi ba face su bukaci shugaban kasa Tinubu ya daina neman sake tsayawa takara karo na biyu."
"Maimakon haka, ya kamata ya yi amfani da sauran lokacin wa'adinsa wajen sake fasalin Najeriya tare da ba ta sabon kundin tsarin mulki, kamar yadda ya dace da dattijon dan siyasa mai tunanin tarihi da makomar al'umma."

Sukar tikitin Muslim-Muslim

NCEF ta sake sukar tikitin Musulmi da Musulmi da Tinubu ya yi amfani da shi a zaben shugaban kasa na 2023.

Kungiyar ta bayyana tikitin a matsayin wanda bai yi la'akari da halin da kasar ke ciki ba, kuma rashin nuna damuwa ne ga mabanbantan bangarorin al'umma.

Kara karanta wannan

APM ta ce Tinubu ya tara malaman addini ya sharara masu karya

Dattawan sun ce an dauki wannan mataki ne a lokacin da 'yan ta'adda ke addabar kasar, yayin da Kiristoci ke fuskantar tashe-tashen hankula, kashe-kashe da sauran munanan ayyuka.

Gargadi ga bangaren shari'a

Kungiyar ta gargadi bangaren shari'a da ya guji duk wani abin da zai nuna son kai wajen yanke hukunci kan rikice-rikicen zabe.

NCEF ta ce Najeriya ta kai wani muhimmin matsayi da ba za ta iya jure nuna bangaranci daga bangaren shari'a ba.

Haka kuma, kungiyar ta bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kare 'yancinta tare da tabbatar da gudanar da sahihin zabe cikin 'yanci da adalci.

Batun karba-karbar mulki

Dangane da tsarin karba-karbar shugabancin kasa tsakanin Arewa da Kudu, kungiyar ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai wajabta tsarin ba.

Sai dai ta ce tsarin yana da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiyar kasa, adalci da bai wa kowane bangare damar shiga cikin shugabanci.

Sanarwar ta ce:

"Saboda haka, ana kira ga masu kishin kasa su goyi bayan dan takara daga Kudu a zaben 2027 domin kammala sauran shekaru hudu na wa'adin yankin."

Kara karanta wannan

'Babu yan bindiga a Niger': Gwamnati ta gano yadda aka samu rashin tsaro

An nemi Tinubu ya hakura da takara
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Keyamo ya hango nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Festus Keyamo, ya bayyana kwarin gwiwar cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 cikin sauki.

Keyamo ya ce bisa la'akari da yanayin siyasa da lissafin karfin kuri'u, zaben shugaban kasa mai zuwa ba zai zama takara ba, illa tamkar nadin sarauta ga Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com