Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Shugabannin Makarantu da Babbar Kyauta
- Gwamnatin jihar Borno ta bai wa shugabannin makarantu motoci saboda ƙwazonsu da gudummawar da suka bayar wajen bunƙasa ilimi
- Kwamishinan ilimi, Lawan Wakilbe, ya ce gwamnatin Babagana Zulum za ta ci gaba da yabawa tare da saka wa ƙwararrun malamai
- Wadanda suka amfana sun ce kyautar za ta ƙara musu ƙwarin gwiwar ci gaba da aiki cikin gaskiya da jajircewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Borno - Gwamnatin jihar Borno ta bai wa shugabannin makarantu uku da suka yi fice motocin aiki domin karrama su bisa ƙwazonsu, jajircewarsu da gagarumar gudummawar da suka bayar wajen bunƙasa ilimi a jihar.
Kwamishinan ilimi, kimiyya, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire na jihar Borno, Lawan Wakilbe, ya miƙa motocin a madadin Gwamna Babagana Zulum.

Source: Facebook
An bayyana cewa bayar da motocin na daga cikin ƙudirin gwamnatin jihar na inganta ƙwazo, ƙara wa malamai ƙwarin gwiwa da kuma ƙarfafa shugabanci a makarantun gwamnati.
Dalilin ba shugabannin motoci
Da yake jawabi yayin bikin miƙa motocin, Wakilbe ya ce karramawar ba wai lada ce kawai saboda shekarun da suka yi suna aiki ba.
Ya ce an karrama shugabannin makarantun ne saboda ƙwarewarsu, jajircewarsu, amfani da sababbin dabaru da kuma tasirin da suka yi a fannin ilimi.
Kwamishinan ya lura cewa duk da matsalolin tsaro da suka daɗe suna addabar sassa da dama na jihar, malamai da shugabannin makarantu da yawa sun ci gaba da sauke nauyin da ke kansu.
A cewarsa, jajircewar malamai da masu kula da makarantu ta taimaka wajen tabbatar da cewa ana ci gaba da koyarwa da karatu duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
Gwamnatin Borno ta yaba wa malamai
Wakilbe ya sake jaddada cewa gwamnatin jihar Borno za ta ci gaba da gano malamai masu ƙwazo, ƙarfafa musu gwiwa da kuma saka musu.
Ya ce malamai masu aiki tuƙuru da jajircewa za su ci gaba da samun karramawar da ta dace da irin gudummawar da suke bayarwa.
“Babu wani malami mai jajircewa da za a bari a baya. Za mu ci gaba da yabawa da saka wa masu ƙwazo saboda malamai su ne ginshiƙin fannin ilimi,” in ji Wakilbe.
Wadanda suka amfana sun yi godiya
Shugabannin makarantun da suka amfana sun nuna matuƙar godiyarsu ga Gwamna Babagana Zulum bisa wannan karramawa.
Sun ce kyautar za ta ƙara musu ƙwarin gwiwar ci gaba da aiki da ƙwazo, riƙon amana da kuma sadaukar da kai wajen sauke nauyin da ke kansu.
Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da suka halarci bikin sun yabawa wannan shiri, suna mai cewa babban mataki ne wajen haɓaka al’adar ƙwazo, ɗaukar alhaki da kuma gasa mai kyau tsakanin malamai.

Source: Original
Sun ƙara da cewa karrama malamai da suka yi fice ba wai kawai yana ƙara wa ma’aikata ƙwarin gwiwa ba ne, har ma yana zaburar da malamai da shugabannin makarantu a faɗin jihar su ƙara ƙoƙari wajen samar da ingantaccen ilimi.
Za a dauki sababbin malamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta fara aikin ɗaukar sababbin malamai 3,050 domin koyarwa a makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandare na gwamnati.
Gwamnatin Zamfara za ta dauki ma'aikatan ne a wani yunƙuri na magance ƙarancin malamai da inganta harkar ilimi a jihar.
Asali: Legit.ng

