Lokaci Ya Yi: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Rasu

Lokaci Ya Yi: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Rasu

  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Ibrahim Aliyu, ya rasu bayan ya yi fama da doguwar jinyar rashin lafiya
  • Marigayin ya yi mataimakin gwamna a gwamnatin tsohon gwamna Saidu Usman Dakingari daga shekarar 2007 zuwa 2015
  • Gwamna Nasir Idris ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masarautar Yauri da jihar Kebbi da Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Ibrahim Aliyu, ya rasu bayan ya yi doguwar jinya, kamar yadda majiyoyin iyalansa suka tabbatar.

Rahotanni sun nuna cewa Alhaji Ibrahim Aliyu, wanda ya yi mataimakin gwamna a gwamnatin tsohon gwamna Saidu Usman Dakingari daga 2007 zuwa 2015, ya rasu ne a jihar Sokoto.

Tsohon mataimakin gwamnan Kebbi ya rasu
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Legit Hausa ta samu rahoton rasuwar marigayi tsohon mataimakin gwamnan na jihar Kebbi ne a ranar Juma'a, 31 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Tsohon minista daga Arewa ya rasu, gwamnonin yankin sun tuna alherinsa

Gwamna Nasir ya yi ta'aziyya

Da yake martani kan rasuwar, gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana alhininsa tare da cewa mutuwar tsohon mataimakin gwamnan babban rashi ce ga masarautar Yauri da jihar Kebbi da ma Najeriya baki ɗaya.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Yahaya Sarki, ya fitar a shafinsa na Facebook Gwamna Idris ya ce marigayi Ibrahim Aliyu na daga cikin fitattun shugabannin da jihar Kebbi ta yi.

Gwamnan ya ce rayuwar marigayin ta kasance cike da hidima ga jama'a ba tare da son kai ba, riƙon amana da jajircewa wajen kyautata al'umma.

Gwamna ya yabawa marigayin

Gwamna Nasir Idris ya ce Ibrahim Aliyu ya yi fice a matsayinsa na ƙwararren ma'aikacin gwamnati, sannan ya taka rawar gani a lokacin da yake mataimakin gwamnan jihar.

Ya ce halin tawali'u da gaskiya da kuma jajircewar marigayin wajen ganin jihar Kebbi ta samu ci gaba sun sa ya samu girmamawa daga jama'a da dama.

Kara karanta wannan

Sardaunan Sokoto, Abubakar Alhaji ya riga mu gidan gaskiya

A cewarsa, marigayin ya bar kyakkyawar gadon jagoranci da hidimar jama'a da za ta ci gaba da zama abin koyi ga al'ummomi masu zuwa.

Gwamnan ya ce:

“Gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jiharmu da kuma jajircewarsa wajen inganta walwalar jama'armu za su ci gaba da zama abin koyi ga al'ummomi masu zuwa.”

Addu'ar Gwamna Nasir Idris ga marigayin

Gwamna Idris ya roƙi Allah ya gafarta wa marigayin tare da ba shi mafificiyar aljanna, Aljannatul Firdaus.

Haka kuma, ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da masarautar Yauri da kuma al'ummar jihar Kebbi.Gwamnan ya roƙi Allah ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi.

Gwamna Nasir Idris ya yi alhinin rasuwa
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Tsohon Ministan kudi ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya (NNGF) ta yi alhini game da rashin da aka yi na tsohon ministan kudi a Najeriya.

Kungiyar ta bayyana alhini kan rasuwar tsohon Ministan Kudi kuma Sardaunan Sokoto, Alhaji Abubakar Alhaji, wanda ya rasu a Abuja.

Ta bayyaa cewa rasuwar Alhaji Abubakar Alhaji babban rashi ne ga iyalansa, al'ummar Sokoto, Arewacin Najeriya da kuma kasa baki ɗaya saboda kwarewarsa da nagartaccen shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng