Ma'aji: An Gano Matsalar Shugaban Masu 'Juyin Mulki' da Rundunar Sojoji, Gwamnati
- Kanar Mohammed Ma’aji ya shaida cewa ya fara tunanin juyin mulki tun 2023 bayan ya gaza samun karin girma zuwa birgediya janar
- Ya ce rashin tsaro, matsalar jin dadin jami'an soja da masu ritaya, da kuma takaicin rasa karin girma suka sa shi da wasu suka farfado da shirin juyin mulki
- Ma'aikatan leken asirin soja sun kama Ma’aji bayan an gayyace shi taron da ya yi zaton za a tattauna karin girmansa, amma aka fara yi masa tambayoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugabam sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki, Kanar Mohammed Ma’aji ya magantu kan zarginsa da ake yi.
Kanal Ma'aji ya bayyana cewa tun shekarar 2023 yake neman karin girma zuwa mukamin Birgediya Janar.

Source: Facebook
Yadda Kanal Ma'aji ke faduwa jarabawa
Bayan ya gaza samun karin girman sau biyu, ya ce ya fara ganin kamar ba zai samu adalci ba, cewar rahoton Premium Times.
A cewar Ma’aji, tun a karshen mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara tattaunawa da wasu kan yiwuwar juyin mulki.
Ma'aji ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro da kuma halin kuncin jami'an soja masu aiki da masu ritaya ne suka kara tunzura shi.
Ya ce ya yi imanin cewa shugabannin rundunar soja sun kasa magance matsalolin jin dadin jami'ai da sojoji. Wannan ne ya sa ya fara neman masu ra'ayi iri daya domin tattauna yiwuwar sauyi a kasar.
Sai dai ya ce wasu rahotanni sun isa ga manyan hafsoshin soja, a shekarar 2023 aka gayyace shi zuwa Hukumar Leken Asirin Tsaro (DIA), inda aka tsare shi na dare guda saboda zargin wasu 'yan siyasa na son amfani da shi wajen tayar da tarzoma a lokacin zaben 2023.
Ma’aji ya ce jami'an tsaro sun kwace wayarsa domin binciken fasaha, amma daga baya aka sake shi tare da ba shi hakuri saboda babu wata hujja da ta tabbatar da zargin da ake masa.

Kara karanta wannan
"Shiri ne": Yadda aka kashe babban soja mahaddacin Kur'ani mai shirin kafa tarihi
Bayan ya sake rasa karin girma a shekarar 2024, ya ce wasu kananan jami'an da ke karkashinsa suka matsa masa lamba su farfado da shirin.
Ya ce sun nuna fargabar cewa idan aka tilasta masa ritaya, za su yi nadamar rashin daukar mataki tun da wuri.

Source: UGC
Juyin mulki: Yaushe aka cafke Kanal Ma'aji?
An kama Ma’aji ne ranar 29 ga Satumban 2025 bayan jami'an soja sun yi amfani da burinsa na samun karin girma wajen jawo shi zuwa wani taro da ya yi zaton za a tattauna makomarsa ta aiki.
Ya ce shugaban rundunar sojin kasa na lokacin, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya kira shi tare da bukatar ya hanzarta zuwa wani gida a Barikin Niger domin tattauna batun karin girmansa.
Ma’aji ya ce bayan sun tattauna kan dalilin da ya sa aka dakatar da karin girmansa, sai shugaban hukumar leken asirin tsaro, Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye, ya iso ya bukaci ya raka shi zuwa hedikwatar DIA domin karbar wani sako.
Ya ce bayan ya isa hedikwatar DIA, an kai shi ofishin Birgediya Janar Nicholas Ashinze, inda aka fara yi masa tambayoyi kan zargin shirin juyin mulki da ya shafi shi da wasu jami'ai.
Da farko ya musanta zargin, amma aka sanar da shi cewa an riga an kama daya daga cikin wadanda ake zargi.
A cikin bayaninsa ga masu bincike, Ma’aji ya roki a yi wa sauran wadanda ake zargi afuwa.
Ya ce sun fahimci kuskurensu, yana mai cewa manufarsu ita ce inganta Najeriya da kuma gyara matsalolin da ke addabar rundunar soja.
Ya kuma bayyana cewa jami'ai da sojoji na fama da tsadar rayuwa, karancin gidaje, da kuma matsalolin walwala.
Juyin mulki: Miliyoyin da malaman Musulunci suka karba
An ji cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa malaman Musulunci sun karbi miliyoyi a yunkurin juyin mulkin da aka yi a Najeriya.
Malaman addinin Musulunci da aka ambata sun shaida wa masu bincike cewa sun yi kokarin hana shi ci gaba da aikata wannan laifi.
Daya daga cikin malaman ya ce ya karbi miliyoyin Naira domin addu'a da ayyukan alheri, yana musanta cewa ya goyi bayan yunkurin.
Asali: Legit.ng

