An Tafka Asara: Yadda Iran Ta Lalata Manyan Kadarorin Amurka a Gabas Ta Tsakiya
- Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta lalata kadarorin sojin Amurka na biliyoyin daloli a yankin Gabas Ta Tsakiya, ciki har da jiragen yaki
- Masana sun kiyasta cewa gyaran wuraren da aka lalata zai iya lashe dala biliyan 5, ban da kudin makamai da jiragen da aka riga aka barnatar
- Akwai damuwa tsakanin 'yan majalisar Amurka kan rashin bayyana hakikanin asarar da aka yi, yayin da Pentagon ke neman karin kasafin kudi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka – Gwamnatin Shugaba Donald Trump tana fuskantar matsin lamba kan gaskiyar irin barnar da dakarun Iran suka yi wa sansanonin sojin Amurka a yankin Gulf.
Rahoto ya nuna cewa, Amurka ta tafka asara mai yawa a yakin da ta yi da Iran, wanda wasu masana ke ganin cewa bai amfani Amurka ba ta kowace fuska.

Source: Getty Images
Girman barnar da Iran ta yi wa Amurka
Binciken da kafar yada labarai ta NBC ta gudanar ya nuna cewa hare-haren da Iran ta kai ya shafi wurare masu muhimmanci kamar hanyoyin tashi da saukar jiragen sama, manyan na'urorin radar, hedkwatar rundunar sojin ruwa, da tsarin sadarwa na tauraron dan adam.
A kasar Kuwait, wani jirgin yakin Iran samfurin F-5 ya fara kai hari a sansanin Camp Buehring tun farkon yakin da ya barke a ranar 28 ga watan Fabrairu 2026.
Haka kuma, harin Iran ya lalata wuraren ajiyar man fetur, asibitoci da wuraren kwanan sojoji asansanin Al Dhafra da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Rundunar sojin ruwa ta biyar ta Amurka da ke Bahrain ma ba ta tsira ba, inda aka kiyasta cewa gyaran hedkwatarsu kadai zai iya lashe dala miliyan 200.
Hukumomin leken asiri na AEI sun rahoto cewa dakarun Iran sun kai hari a sansanin Ali Al Salem da ke Kuwait, da hanyar jiragen sama a Al Udeid da ke Qatar, har ma da rumbun ajiyar makamai a wani sansanin soji da ke arewacin kasar Iraki.
Asarar makamai da kudin gudanar da yaki
Baya ga sansanonin, Amurka ta rasa muhimman makamai da jirage, kamar yadda rahoton The Hill ya nuna.
Rahotanni sun nuna cewa akalla jirgin yaki daya, da jirage marasa matuka samfurin MQ-9 Reaper guda 12, da jiragen dakon mai na MC-130, da jiragen helikwafta duk suka lalace.
A watan Maris ne ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta kiyasta cewa kwanaki shida na farko na yakin Iran sun lashe sama da dala biliyan 11.3, ba tare da hada kudaden da za a kashe wajen gyaran sansanonin da aka ruguza ba.
Wani babban jami’i a majalisa wanda ya tattauna da jaridar The New York Times ya bayyana cewa asarar tana da girman gaske:
Majalisar Amurka ma ta nuna bacin ranta kan yadda fadar White House ta ki ba su cikakkun bayanai kan yadda aka kashe dala biliyan 5.6 wajen sayen makamai a cikin kwanaki biyu kacal na farkon fadan.

Source: Getty Images
Kalubale ga gwamnatin Donald Trump
Yayin da yakin ke ci gaba da ci, ana samun takun-saka tsakanin fadar White House da 'yan majalisa wadanda ke bukatar gaskiya kan asarar rayuka da dukiyoyin kasar.
Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta nemi a kara mata kasafin kudi mafi girma a tarihi, amma ma'aikatan majalisa sun ce ba za su amince ba har sai sun fahimci inda kudaden da aka kashe a baya suka tafi.
Iran ta mika sabon tayin sulhu ga Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, bayan ta ja kafa na ƴan kwanaki, Iran ta fara nuna alamun don a koma teburin tattaunawa da Amurka don a sasanta rikicin yankin.
Babban abin da Iran ta fara yi shi ne mika sabon tayin sulhu ga Amurka domin buɗe mashigar Hormuz da sojojin Amurka suka yi wa tsinke.
Daga cikin abin da sabon tayin ya ƙunsa akwai jinkirta tattaunawar nukiliya har sai an ɗage takunkumin da Amurka ta ƙaƙabawa Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


