Trump Ya Ja da Baya kan Shirin Gwabzawa da Dakarun Iran a Hormuz

Trump Ya Ja da Baya kan Shirin Gwabzawa da Dakarun Iran a Hormuz

  • Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta dakatar da aikin bude mashigar Hormuz da karfi da ke da nufin jagorantar jiragen kasuwanci su ratsa ta wajen
  • Sanarwar da Donald Trump ya fitar ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce aikin yaƙi da Iran ya ƙare
  • Wasu bayanai da aka samu daga jami'an gwamnatin kasar Iran ya nuna Tehran ta caccaki Donald Trump kan cewa ya ja da baya kan shirin da ya yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Trump ya dakatar da shirin Amurka na kutsawa mashigar Hormuz domin ƙoƙarin cimma yarjejeniya da shugabannin Iran.

Shugaban ya ce an dakatar da shirin raka jiragen ruwa a Hormuz ne domin a ga ko za a kammala yarjejeniya da Iran kuma a rattaba hannu a kanta.

Kara karanta wannan

Minista a gwamnatin Trump ya fadi kasar da ke da ikon bude mashigar Hormuz

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump a wajen wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dalilin ja da baya da Trump ya yi

Al Jazeera ta rahoto Shugaban Amurka ya bayyana cewa an dakatar da aikin soja na fitar da jiragen da suka makale daga mashigin Hormuz na ɗan lokaci.

Ya ce an ɗauki matakin ne bisa roƙon Pakistan da wasu ƙasashe da kuma ganin cewa an samu babban ci gaba wajen cimma cikakkiyar yarjejeniya da wakilan Iran.

“Mun amince tare cewa duk da cewa toshewar mashigar zai ci gaba da aiki yadda yake, za a dakatar da shirin raka jirage na ɗan lokaci domin a ga ko za a iya kammala yarjejeniyar kuma a sanya hannu,”

In ji shi.

Sanarwar Trump ta zo ne yayin da tashin hankali ke ƙaruwa a yankin Tekun Fasha, inda sojojin Amurka suka ce sun lalata wasu jiragen Iran a mashigar Hormuz, tare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa.

Wasu jirage na tafiya a Hormuz
Yadda wasu jirage ke tafiya ta kusa da mashigar Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A daya bangaren kuma, kasar UAE ta ce ta dakile hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa daga Iran na kwanaki biyu a jere.

Kara karanta wannan

Amurka ta kai hari kan jiragen Iran, dakarun Trump sun kashe mutane

Martanin Iran ga Amurka

A nata ɓangaren, rundunar IRGC ta Iran ta fitar da sabuwar taswirar mashigar, inda ta faɗaɗa yankin da take iko da shi, tare da gargadin jiragen ruwa da su bi hanyoyin da ta tanada ko kuma su fuskanci martani mai tsauri.

CNN ta wallafa cewa gwamnatin kasar Iran ta ce shugaba Donald Trump ya ja da baya daga aikin bude Hormuz da ya ce zai yi.

Iran ta yi magana tana cewa hakan ya biyo bayan gargadin da ta yi game da tarwatsa duk wani jirgin da ya yi kokarin kutsawa da ta mashigar.

Amurka ta farmaki jiragen Iran

A wani labarin, mun kawo muku cewa sojojin Amurka sun kai farmaki kan wasu jiragen ruwan Iran na fararen hula a kusa da Hormuz.

Gwamnatin Iran ta sanar da cewa Amurka ta kashe mutum biyar a cikin wadanda aka dauko a cikin jiragen ruwan, inda ta ce hakan zalunci ne.

Haka zalika, Iran ta nuna cewa Amurka ta yi karya game da cewa ta kai hari kan rundunar sojinta da ake ayyukan tsaro a cikin teku.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng