Sharadin Trump ga Iran yayin da Ya Ke Shirin Afkawa Kasar da Yaki Karo na 2
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake yin barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran yayin da maganar sulhu ke rugujewa
- Trump ya bayyana cewa yana nazarin sabon tayin yarjejeniya daga Iran yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan ƙarshen yaƙi da buɗe mashigar Hormuz
- Rahotanni sun ce shugaban Amurka ya samu bayanin sababbin tsare-tsaren kai hari kan Iran daga kwamandan CENTCOM yayin da rikici ke ƙara tsananta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa gwamnatinsa na iya sake kai hare-haren soji kan Iran.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Donald Trump ya bayyana haka ne da cewa zai kai harin ne idan ƙasar ta aikata abin da ya kira “mummunan hali”.

Source: Getty Images
Trump ya yi wannan bayani ne yayin tattaunawa da manema labarai a West Palm Beach da ke jihar Florida ranar Asabar 2 ga watan Mayun 2026 da muke ciki, cewar Reuters.

Kara karanta wannan
Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka
Trump ya magantu kan kai hari Iran
Da aka tambaye shi abin da zai iya janyo sabon harin soja, shugaban ya ƙi bayyana dalla-dalla, yana mai cewa lokaci ne zai nuna abin da zai faru.
Ya ce:
"Idan Iran ta “yi abin da bai dace ba”, akwai yiwuwar Amurka ta sake ɗaukar matakin soji a kan jamhuriyar Musulunci."
Rahotanni sun nuna cewa duk da ci gaba da musayar shawarwari tsakanin Amurka da Iran, gwamnatin Trump na duba yiwuwar sake kai hare-hare domin karya matsayar Tehran.
Iran ta gabatar wa Amurka da sabon tsarin yarjejeniya mai maki 14 domin kawo ƙarshen yaƙi da sake buɗe mashigar Hormuz da aka rufe wand ya jawo matsala a tattalin arzikin duniya.
Majiyoyi biyu sun bayyana cewa Iran ta ba Amurka wa’adin wata guda domin cimma yarjejeniya kan kawo ƙarshen killacewar ruwa da yaƙin Iran da Lebanon.
Bayan cimma wannan yarjejeniya ne za a sake shiga wata tattaunawa ta daban kan shirin nukiliyar Iran da sauran matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan
Iran ta karyata Amurka kan asarar da Trump ya yi a yaƙin Isra'ila, ta fadi adadin dalolin

Source: Twitter
Yadda Trump ya samu bayanai kan hari
Rahoton ya kuma nuna cewa Trump ya samu bayani daga kwamandan CENTCOM, Admiral Brad Cooper, kan sababbin shirye-shiryen kai hari kan Iran.
An bayyana cewa Cooper ya tafi yankin Gabas ta Tsakiya kuma ya gana da sojojin Amurka da ke cikin jirgin ruwa na USS Tripoli a Tekun Larabawa.
Bayan cimma wannan yarjejeniya ne za a sake shiga wata tattaunawa ta daban kan shirin nukiliyar Iran da sauran matsalolin tsaro, cewar Al Jazeera.
Iran ta zargi Amurka da karya
Kun ji cewa ce kasar Iran ta zargi Amurka da karya kan kudin da aka kashe yayin yakin Jamhuriyar Musulunci da Isra'ila.
Iran ta ƙaryata wasu rahotanni kan asarar da Donald Trump ya yi tana cewa gwamnatinsa ta boye hakikanin adadin kuɗin da ya yi asara.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce yakin ya jefa iyalan Amurka cikin karin kashe kudade, yana cewa kowane gida na biyan dala 500.
Asali: Legit.ng