Iran Ta Kai Kazamin Hari, Ta Latata Jiragen Yaki da Kashe Sojojin Amurka
- Rundunar IRGC ta Iran ta yi iƙirarin cewa ta kai hari da makamai masu linzami kan sansanin sojin saman Al-Azraq da ke Jordan, inda ta lalata jiragen yaƙin Amurka F-35 uku
- Iran ta ce harin martani ne ga hare-haren da Amurka ta kai kan wasu gidaje biyu a tsibirin Qeshm, tare da zargin cewa jami'an soja da ma'aikatan kula da jiragen sun mutu.
- Sai dai gwamnatin Jordan ta ce dakarunta sun kakkabo makamai masu linzami biyar da aka harba daga Iran, yayin da babu wata sanarwa daga Amurka da ta tabbatar da iƙirarin Tehran.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran, Iran – Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi iƙirarin cewa ta lalata jiragen yaƙin Amurka kirar F-35 guda uku bayan kai hari da makamai masu linzami kan sansanin sojin saman Al-Azraq da ke gabashin ƙasar Jordan.
Rundunar ta ce harin ya kuma jikkata wasu jirage uku na F-35 tare da kashe wasu jami'an soja da ma'aikatan fasaha da ke kula da jiragen.

Source: Getty Images
Anadolu ta rahoto cewa IRGC ta bayyana harin a matsayin martani ga harin da Amurka ta kai kan wasu gidaje biyu da ke tsibirin Qeshm a kudancin Iran.
An lalata jiragen Amurka
A cikin sanarwar da ta fitar, IRGC ta ce rundunar sararin samanta ta harba makamai masu linzami kan wurin da ake ajiye jiragen F-35 da kuma hangar ɗin kula da su a sansanin Al-Azraq.
Ta ce:
"Mun lalata jiragen F-35 guda uku gaba ɗaya, sannan muka yi wa wasu uku mummunar ɓarna."
Rundunar ta ƙara da cewa wasu jami'an sojan Amurka da ma'aikatan kula da jiragen sun mutu a harin, tana mai cewa yankin Gabas ta Tsakiya ba wuri ba ne ga sojojin Amurka.
Jordan ta kakkabo makamai
A nata ɓangaren, rundunar sojin Jordan ta sanar da cewa ta kakkabo makamai masu linzami biyar da aka harba daga Iran zuwa cikin ƙasar.
Hakan ya sa wannan ya zama rana ta huɗu a jere da Jordan ke sanar da dakile makamai ko jirage marasa matuƙa da aka harba daga Iran.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga rundunar sojin Amurka da ta tabbatar da iƙirarin Iran cewa an lalata jiragen F-35 ko kuma an kashe jami'anta a harin.

Source: Getty Images
Iran na ci gaba da fitar da mai
A wani ɓangaren kuma, rahotanni sun nuna cewa jirgin dakon ɗanyen man Iran mai suna Humanity ya ci gaba da zirga-zirga ta mashigin Malacca kafin ya nufi gabar tekun Malaysia.
Masana harkokin tsaron teku sun bayyana cewa ana zargin jirgin ya kashe na'urar tantance matsayinsa (AIS) domin sauke ɗanyen mai zuwa wani jirgi a tsakiyar teku, kafin daga bisani a kai shi kasar China.
Al Jazeera ta wallafa cewa ana kyautata zaton China ce ke karɓar mafi yawan ɗanyen man Iran duk da takunkumi da rikicin da ake ciki.
An farmaki tankar Amuka
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Masar ta tabbatar da cewa harin jirgi marar matuƙi ne ya haddasa gobarar da ta tashi a wasu jiragen iskar gas biyu a tashar jiragen ruwa ta Damietta.
Bayan sanar da cewa daya jirgin na Amurka ne, gwamnatin ta ce bincike na ci gaba da gano waɗanda suka kai harin, tare da ɗaukar matakan kare tsaron ƙasar.
Lamarin ya ƙara tayar da hankula kan yiwuwar rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka ya bazu zuwa ƙarin ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

