Amurka Ta kai Hari kan Jiragen Iran, Dakarun Trump Sun Kashe Mutane
- Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar Amurka sun kai hari kan wasu jiragen ruwa da suka nufi Iran a kusa da mashigar Hormuz
- Gwamnatin Iran ta tabbatar da kai harin, inda ta ce an kashe wasu daga cikin fararen hula da ke cikin jirgin ba tare da sun aikata laifi ba
- Hakan na zuwa ne yayin da lamura ke kara zafi tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya, musamman kan mashigar ruwan Hormuz
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Wata majiyar soja ta ce Amurka ta kai hari kan wasu ƙananan jiragen ruwa biyu na daukar kaya na fararen hula da ke kan hanyarsu daga gabar tekun Oman zuwa gabar Iran.
Rahotannin da suka fito daga gwamnatin Iran sun nuna cewa lamarin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyar da ke cikin jiragen.

Source: UGC
Harin Amurka kan jiragen Iran
Rahoton Merhr News ya ce majiyar ta karyata zargin da Amurka ta yi cewa ta kai hari kan jiragen ruwan rundunar IRGC, tana mai cewa:
“Maimakon kai hari kan jiragen IRGC, Amurka ta aikata mummunan laifi ta hanyar bude wuta kan wasu kananan jiragen dauke da kayan fararen hula.”
Ta kara da cewa bayan bayanin da Washington ta fitar, an tuntubi majiyoyin yankin domin tabbatar da hakikanin abin da ya faru, ganin cewa babu wani jirgin yakin IRGC da aka kai wa hari.
“Bincike ya nuna cewa a zahiri dakarun Amurka ne suka kai hari kan kananan jiragen kaya guda biyu na fararen hula.
"Jiragen suna kan hanyarsu daga garin Khasab da ke gabar Oman zuwa gabar Iran. Harin ya yi sanadin mutuwar fasinjoji fararen hula guda biyar,”
In ji majiyar.
Matsayar Iran kan harin Amurka
Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa majiyar ta jaddada cewa dole ne a daurawa Amurka alhakin laifin kashe fararen hula ba tare da laifi ba.
Ta danganta wannan hari da yadda Amurka ke aikata abubuwa cikin gaggawa da rashin tsari, sakamakon tsoro da firgici da ta ke ciki tun bayan gargadin da Iran ta yi kan jiragen ruwa masu shiga yankin Tekun Farisa da mashigar Hormuz.
An dade ana samun tashin hankali a yankin Tekun Farisa da mashigar Hormuz tun daga ranar 28 ga Fabrairun 2026, lokacin da Amurka da Isra’ila suka fara hari kan Iran ba tare da wani dalili ba.

Source: Getty Images
Yanzu Iran na dagewa kan ci gaba da rike ikon mashigar Hormuz tare da karbar kudin wucewa a matsayin diyya kan barnar da Amurka da Isra’ila suka yi mata.
An kai hari matatar mai a UAE
A wani rahoton, kun ji cewa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ce Iran ta kai hari da jirgi marar matuki kan daya daga cikin tankokin man ta.
Mahukuntan UAE sun ce hare-haren sun haddasa babbar gobara a wata muhimmiyar matatar mai a yankin Fujairah da ke gabashin kasar.
Sai dai a martanin da gwamnatin kasar Iran ta yi, ta bayyana cewa ba ta da hannu a harin, tare da cewa Amurka za a zarga da lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

