Muhammad Malumfashi
20409 articles published since 15 Yun 2016
20409 articles published since 15 Yun 2016
Dazu aka ji Gwamnatin Kano za ta cika alkawarin da tayi wajen ganin an yi adalci a shari’ar Hanifa. Abdullahi Ganduje zai sa hannu ba tare da bata lokaci ba.
Babban ‘Dan Sandan Najeriya ya lashe gasa a Amurka, ya kawo tutar Judo gida. Disu Olatunji Rilwan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne da zai yi ritaya a 2026.
Gwamnoni sun ba gwamnatin tarayya shawarar ta biya ma’aikatan da suka kai shekara 50 a Duniya kudin fansho domin su ajiye aikinsu, sannan a cire tallafin mai.
Benjamin Kalu yana ganin ba zai yiwu a iya kammala tsige Muhammadu Buhari zuwa Mayu ba, an ji Kalu yana cewa lokacin da ake da shi ba zai isa ayi nasar ba.
Ba tare da sani ko nuna sabo ba, za a ji Yadda KASTELEA suka tare motar Bashir El-Rufai. Hakan na zuwa ne bayan an kama 'dan jarida ya saba doka a jihar Legas.
An bayyana wani Ministan Buhari da yake yi wa Bola Tinubu zagon-kasa a 2023. Ana tuhumar Ministan cikin gida da hannu a nasarar da PDP ta samu a zaben 2022.
Tsohon Sanata ya gargadi ‘Yan PDP a kan yunkurin tunbuke Shugaban kasa. Shehu Sani yace Sanatocin PDP su ajiye batun tsige Buhari a gefe, ba zai taba yiwuwa ba.
Shugaban kasar Nijar ya karrama Aliko Dangote da wasu Gwamnonin Najeriya. Mohammed Bazoom ya kuma bada lambar yabo ga Aliko Dangote da Abdussamad Isiyaka Rabiu.
Tun da aka harbi mutane aka ji jirgin Warri-Itakpe ba zai rika tsayawa a Ajaokuta ba. Jirgin Legas zuwa Kano ba zai rika tashi ba saboda ta'adin ‘yan bindiga.
Muhammad Malumfashi
Samu kari