Tsohon Sanata yayi Gargadi Kan Tunbuke Shugaban kasa, Ya Hango Abin da Zai faru

Tsohon Sanata yayi Gargadi Kan Tunbuke Shugaban kasa, Ya Hango Abin da Zai faru

  • Shehu Sani ya bada shawara cewa ayi watsi da maganar tunbuke shugaban kasa a halin yanzu
  • A matsayin wanda ya san Majalisar tarayya, Shehu Sani yace lokaci ya kurewa Sanatocin PDP
  • Kwamred Sani yace maganar ba za ta je ko ina ba, don haka zai fi kyau a maida hankali a zabe

Kaduna - Tsohon Sanata a Najeriya, Shehu Sani ya yi kira ga ‘yan hamayya da ke majalisar tarayya da su maida hankalinsu ne a game da babban zabe.

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa tsige shugaban kasa ba zai yiwu ba, don haka ‘yan majalisar su daina bata lokacinsu, Premium Times ta kawo rahoton.

Kamar yadda yake cewa, yana goyon bayan a tunbuke Muhammadu Buhari, amma sam dokar kasa ba za ta bari a iya cin ma wannan kafin zabe mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Na Fadawa Tinubu Ban Bukatar Komai a Gwamnatinsa, Na Bada Dalilina

Wani dalilin watsi da batun kuma shi ne shugabannin majalisa ba za su goyi bayan hakan ba, baya ga cewa wannan yunkuri yana bukatar lokaci mai tsawo.

Tsohon ‘dan takaran gwamnan yake cewa hakan zai yi wahala domin majalisa na shirin tafiya hutu, kuma ko an dawo, ba za a iya samun duka Sanatoci ba.

A maida hankali kan 2023

"A irin wannan lokaci, abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda za a kifar da jam’iyyar mai-ci, duk wani abin dabam kuma zai dauke hankali ne.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasa
Shugaban kasar Najeriya @MBuhari
Asali: UGC

“Shugaban PDP (Iyorchia Ayu) tsohon Sanata ne. Ya san aikin majalisar tarayya. Ina tunani ya kamata ne ya damu da yadda za a lashe zabe.”
“Bata lokaci a game da tsige shugaban kasa zai iya jawo matsala a zabe mai zuwa. Na yarda a tsige shugaban kasa yau idan da babu wata matsala."

Kara karanta wannan

Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

"Idan aka duba tsarin dokar, za a dauki watanni, kuma shugabannin majalisa; Ahmad Lawal da Femi Gbajabiamilla na tare da gwamnati.
A karshe dai bata lokaci kurum za ayi a banza." - Sanata Shehu Sani

A tsige Shugaban kasa ko kuwa?

Kwamred Shehu Sani ya yi wannan jawabi ne a wani shiri da Premium Times ta gabatar a dandalin Twitter a kan maganar tunbuke shugaban Najeriyan.

Tsohon Sanatan na Kaduna, shugaban Enough is Enough (EiE), Yemi Adamolekun, Kakakin PDP, Chinwe Nnorom da mutum sama da 3000 sun halarci shirin.

An karrama 'Yan Najeriya

Ku na da labari cewa a wani taro na musamman da aka yi a babban birnin Yamai, Mohammed Bazoom ya bada lambar yabo ga wasu Gwamnonin Najeriya.

Shugaban Nijar, Mohammed Bazoom ya karrama Aliko Dangote, Abdussamad Rabiu da kuma hadimin shugaban Najeriya, Ambasada Lawal Abdullahi Kazaure.a

Asali: Legit.ng

Online view pixel