Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Nadin Mukami da Zai Taba Rayuwar Matan Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Nadin Mukami da Zai Taba Rayuwar Matan Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Adedayo Laniyi a matsayin shugaba kuma babbar daraktar cibiyar bunkasa mata ta Maryam Babangida
  • Rahoto ya nuna cewa nadin zai fara aiki daga ranar 18 ga Afrilu, 2026 na tsawon wa’adin shekaru hudu kamar yadda doka ta tanada
  • Tinubu ya kuma amince da kafa sabuwar majalisar gudanarwa domin inganta harkokin bunkasa mata da daidaito tsakanin jinsi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Adedayo Laniyi a matsayin Darakta-Janar kuma babbar shugabar cibiyar Maryam Babangida ta kasa don bunkasa mata.

Nadin Adedayo Laniyi a matsayin shugabar cibiyar MBNCWD zai fara aiki daga ranar 18 ga watan Afrilu, 2026 na wa’adin farko na shekaru hudu, kamar yadda sanarwa ta nuna.

Kara karanta wannan

Tinubu ya aika sako ga 'yan APC ana shirin fara zaben fitar da gwani

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Adedayo Laniyi a matsayin shugabar cibiyar MBNCWD
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na sanya hannu kan wasu takardu. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya nada shugabar MBNCWD

An sanar da nadin ne cikin wata takarda da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya sanya wa hannu, a cewar jaridar Punch.

Jaridar ta ruwaito cewa babban sakataren ofishin ayyuka na musamman, Ibrahim Kana ne ya fitar da takardar a ranar Alhamis, 14 ga Mayun 2026.

A cikin wata sanarwa da shugaban yada labarai da hulda da jama’a na cibiyar MBNCWD, Chris Ugwuegbulam ya fitar ranar Alhamis, ya ce nadin ya yi daidai da sashe na 7 (1) da (3) na dokar gyaran cibiyar bunkasa mata ta shekarar 2023.

"Shugaban kasa ya amince da nadin Adedayo Benjamin Laniyi tare da mambobin majalisar gudanarwar cibiyar domin jagorantar cibiyar na tsawon shekaru hudu.
"Nadin, wanda ya fara aiki daga ranar 18 ga Afrilun 2026, ya yi daidai da sashe na 7 (1) da (3) na dokar gyaran cibiyar bunkasa mata ta shekarar 2023."

- Chris Ugwuegbulam.

Kara karanta wannan

Atiku ya dura kan Tinubu da ƴan bindiga suka kashe tsohon ɗan majalisar Jigawa

An kafa majalisar gudanarwar MBNCWD

Shugaba Tinubu ya kuma amince da kafa sabuwar majalisar gudanarwar cibiyar inda aka nada Princess Joan Jummai Idonije a matsayin shugaba, kamar yadda sanarwar ta nuna.

Sauran mambobin majalisar sun hada da Lois Auta, Jamila Sarki, Aisha Baiyee, Jumoke Okoya-Thomas da kuma Princess Anne Agom-Eze.

Kafar watsa labarai ta TVC News ta ruwaito cewa shugaban kasar ya taya sabuwar shugabar cibiyar da sauran mambobin majalisar murna tare da yi musu fatan nasara a ayyukansu.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Adedayo Laniyi a matsayin shugabar cibiyar MBNCWD
Adedayo Laniyi, wadda Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadinta a matsayin shugabar cibiyar MBNCWD. Hoto: @laexjules
Source: Twitter

Ayyukan cibiyar Maryam Babangida

An kafa cibiyar Maryam Babangida ta bunkasa mata ne domin karfafa mata, samar da daidaito tsakanin jinsi da kuma bunkasa tattalin arzikin mata a Najeriya.

Cibiyar na kuma gudanar da bincike, horarwa da wayar da kai kan batutuwan da suka shafi mata da cigabansu a fadin kasar nan.

Tinubu ya nada sabon mai ba shi shawara

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa (Mai Ritaya) a matsayin mai bashi shawara kan tsaron cikin gida.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa tarihi, ya kirkiri sabon ofishi a fadar shugaban kasa kan tsaro

Janar Famadewa ya yi aiki na shekaru sama da 30, inda ya taka rawar gani wajen kafa cibiyar tattara bayanan sirri (IFC) a ofishin NSA.

Babban aikin da ke gaban sabon mashawarcin shi ne samar da dabarun tunkarar barazanar tsaro ta hanyar amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com