Tinubu ya yi Alkawarin ba ni Mukami, Amma Na Dawo Wajen Atiku inji Kakakin PDP
- Hon. Daniel Bwala ya yi magana a game da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP
- Bwala ya bayyana cewa ba kwadayin mukamin Atiku Abubakar ya sa shi barin tafiyar APC ba
- ‘Dan siyasar ya yi Allah-wadai da gwamnatin APC, yace jam’iyyar ba ta cika alkawarun ta ba
Abuja - Mai magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP, Daniel Bwala ya bayyana cewa ya yi watsi da tayin Bola Tinubu.
A ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022, Daniel Bwala ya yi hira da Channels TV, ya nuna cewa ba neman mukami ya sa ya koma jam’iyyar PDP ba.
Tsohon jigon na jam’iyyar APC yake cewa akasin abin da wasu ke tunani, bai bar APC saboda kwadayin samun mukami a tafiyar Atiku Abubakar ba.
“Wani yace ‘na tafi saboda ina son mukami wajen Atiku’. Abin da ba su sani ba shi ne na bar kujerar da ‘dan takaran APC, Tinubu ya yi mani alkawari.
Zai ba ni mai magana da bakin takarar shugaban kasa. Wadannan alkawari ne da ya yi mani kai-tsaye a lokacin da na hadu da shi a cikin motarsa.”
Premium Times ta rahoto Bwala yana cewa Tinubu da gaske yake domin har gwamnoni sun gagara sa shi ya karya alkawarin mukamin da ya yi masa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bwala wanda ya taba rike mukami a majalisar NWC na jam’iyyar APC mai mulki yake cewa akwai wadanda sun san da wannan magana da aka yi.
Baya ga haka, ‘dan siyasar yace ta fuskar tattalin arziki, yayi babban rashi da ya fice daga APC. A cewarsa ya koma PDP domin ya samu natsuwar zuciya.
A hirar da aka yi da shi a gidan talabijin, Bwala yake cewa gwamnatin APC ta gaza cika alkawuran da tayi wa al’umma bayan kusan shekaru bakwai a kan mulki.
Rahoton yace Bwala ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari a kan yajin-aikin da ake yi jami’o’i, yace abin tambaya shi ne gaba aka yi ko baya a yau.
Daga cikin abin da Bwala ya tattauna a hirar akwai tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a APC, yace ba ayi wa duk kiristocin da ke rayuwa Najeriya adalci ba.
Ana cikin matsala - Sanusi II
Dazu aka ji labari Muhammadu Sanusi ya jero matsalolin Najeriya kama daga karuwar rashin tsaro, masifar talauci, da hauhawar farashin kaya a kasuwa.
Muhammadu Sanusi wanda ya rike CBN yace Gwamnatin APC tana tunanin za a yaba mata bayan ta bar mulki, duk da barnar da aka tafka a shekaru bakwai.
Asali: Legit.ng