Rashin Kudi Ya Jawo Gwamnoni Sun Ce A Kori Ma’aikata, a Tsuke Bakin Aljihu Kyam

Rashin Kudi Ya Jawo Gwamnoni Sun Ce A Kori Ma’aikata, a Tsuke Bakin Aljihu Kyam

  • Gwamnonin Najeriya sun ba gwamnatin tarayya shawara ta kori ma’aikatan da suka kai shekara 50
  • An bada shawarar a biya ma’aikatan kudi domin su ajiye aiki, sannan ana so a janye tallafin man fetur
  • Wasu shawarwarin da aka kawo sun hada da ruguza SIP da rage kudin kwangilolin ‘Yan majalisa

Wani rahoto na musamman da Premium Times ta fitar a ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022, yace an kawo shawarar a sallami ma’aikatan da suka kai 50.

Gwamnoni sun yi kira ga Muhammadu Buhari ya yi hakan lura da yadda ake fama da matsin lambar tattalin arziki, da nufin hakan zai magance rashin kudi.

Wadanda suka halarci wannan zama sun shaidawa jaridar cewa gwamnonin sun nuna damuwa kan halin tattalin arzikin da kasar nan ya samu kan shi a yau.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi shugaban 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

Ma’aikatan gwamnatin tarayya ba su wuce 89, 000 ba, amma za su lakume N4.1tr daga kasafin kudin bana. Albashi da alawus na ma’aikatan zai ci kusan 25%.

Hakan ta sa gwamnonin su ka bada shawarar a sallami ma’aikatan da shekarunsu sun kai 50. Ba za a iya cewa ga abin da masu shekarun nan suke karba ba.

Jerin shawarwarin NEC

Rahoton yace gwamnonin sun nemi a janye tallafi man fetur, ayi watsi da tsare-tsaren SIP da NPRGS, sannan a rage kwangilolin da ake ba ‘yan majalisa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buhari
Shugaba Buhari a wani taro Hoto: Buhari Sallau Online
Asali: Facebook

Wata shawara daga bakin gwamonin ita ce a tabbata an gama aikin matatar Dangote, sannan a dage da hako mai da gas yayin da ake rikicin Rasha da Ukraine.

Baya ga haka gwamnonin sun nemi a canza yadda ake karbar haraji, sannan a hana ma’aikatu fita kasashen wajen na tsawon shekara daya domin rage facaka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mazauna Abuja suka dage dole Buhari ya sauke ministansa da mai ba shi shawara

Kwamitin Stephen Oronsaye

Wadannan gwamnoni sun kuma yi kira ga Mai girma Buhari ya dabbaka shawarwarin da kwamitin Stephen Oronsaye ya taba ba Gwamnatin Jonathan.

Kwamitin Stephen Oronsaye ya nemi a hade duk ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati da suke yin aiki iri daya da juna, hakan zai sa a rage kashe kudi.

Bisa dukkan alamu babu kan ta

Ganin gwamnonin jihohi sun fara bada irin wadannan shawara ya nuna kasar na cikin matsala. Abin ya kai ana so a zaftare gibin da ke cikin kasafin kudi.

A makon nan aka samu labari cewa asusun kudin kasar wajen Najeriya ya yi kasa. Daga Dala biliyan 35, abin da ya rage a asusun yanzu bai kai rabin hakan ba.

Har ila yau, an ji cewa asusun rarar man Najeriya ya kusa komawa kar-kaf. Daga Dala miliyan 35.37 da ke ajiye kwanaki, yanzu fam $376,655 rak suka rage.

Kara karanta wannan

Farashin Man fetur: Har Yau Ba Mu Kara Sisin Kobo Kan N165 ba Inji Gwamnati

Asali: Legit.ng

Online view pixel