Shugaban Kasar Nijar ya Karrama Aliko Dangote, Wasu Gwamnonin Arewa 3

Shugaban Kasar Nijar ya Karrama Aliko Dangote, Wasu Gwamnonin Arewa 3

  • Gwamnatin Mohammed Bazoum ta karrama wasu shugabannin Najeriya a babban birnin Yamai
  • Gwamnonin jihohin Zamfara, Jigawa da Kebbi su na cikin wadanda aka karrama a kasar Nijar
  • Shugaban Jamhuriyyar ta Nijar ya kuma bada lambar yabo ga Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Niger - Shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar, Mohammed Bazoum ya karrama wasu daga cikin manyan Najeriya da lambar yabo na girmamawa.

Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 3 ga watan Agusta 2022, wadanda Mohammed Bazoum ya karrama sun hada da Gwamnoni uku.

Mai girma Mohammed Bazoum ya bada lambar yabo ga Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, da Abubakar Badarun jihar Jigawa.

Sannan an karrama Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu a kasar makwabtar.

An karrama manyan 'Yan kasuwa

Jaridar tace Mohammed Bazoum ya bada lambar yabo ga shugaban kamfanonin Dangote da BUA, Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Abdussamad Rabiu.

Kara karanta wannan

Elrufai Ya Ce APC ta Riga Ta Nada Darakata Janar Na Kamfen Din Takarar Tinubu Da Shettima

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na karshe a jerin mutanen Najeriyan da aka karrama a birnin Niamey shi ne Ambasada Lawal Abdullahi Kazaure wanda hadimi ne a Aso Villa.

Shugaban Kasar Nijar
Mohammed Bazoom da wadanda aka ba lambar yabo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci Gwamnonin da aka karrama duk sun fito ne daga Arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ke iyaka da Jamhuriyyar Nijar.

Aliko Dangote ya yi fice

Rahoton Premium Times yace an ba Aliko Dangote lambar Commander of the Order of Merit of Niger ne saboda irin kasuwancin da yake yi a kasar Nijar.

Gwamnatin Bazoum ta yaba da yadda Attajirin Afrikan yake taimakawa kasar da dukiyarsa.

Gidauniyar Aliko Dangote Foundation ta bada gudumuwa wajen inganta lafiyar al’umma da kuma yin rigakafi a mawakbta; Jamhuriyyar Nijar da Chadi.

A baya an taba ba Aliko Dangote lambar yabon National Order of Valour a Kamaru da kuma lambar National Order of the Republic of Benin a Jamhuriyyar Benin.

Kara karanta wannan

Tinubu, Dangote, Gwamnoni Da Sauran Manyan Masu Fada Aji Da Suka Halarci Auren Diyar Shettima

Karancin abinci a Najeriya

Kwanakin baya kun ji labari cewa Majalisar wakilan tarayya ta hango yiwuwar wasu Jihohi su auka cikin matsin yunwa nan gaba a wasu jihohi 16.

Kwamitin harkokin noma a majalisar tarayya sun bukaci a fara daukar matakin da ya kamata. Hon. Rimamnde Shawulu ne ya bada wannan shawarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel