Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Yi Martani kan 'Ganawa' da Netanyahu Ana tsaka da Yakin Iran

Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Yi Martani kan 'Ganawa' da Netanyahu Ana tsaka da Yakin Iran

  • Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi martani kan rahoton cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gana a boye da shugaban kasar
  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa Netanyahu ya hana da Shugaba Mohammed bin Zayed Al Nahyan yayin rikicin Iran
  • Ma’aikatar harkokin wajen UAE ta bayyana cewa dangantakarta da Isra’ila a bayyane take, tana mai cewa babu wata yarjejeniya ta sirri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dubai - Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi karin haske kan rahoton da ake yaɗawa kan ziyarar Benjamin Netanyahu a kasar.

Rahoton ya ce Firayim ministan Isra'ila ya gana da Shugaban UAE, Mohammed bin Zayed Al Nahyan yayin rikicin Iran.

UAE ta musanta ganawa da Netanyahu
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da shugaban UAE, Mohammed bin Zayed Al Nahyan. Hoto: Marc Israel SELLEM/POOL/AFP, Sefa Karacan/Anadolu.
Source: Getty Images

Kasar ta musanta ikirarin cewa Netanyahu ya gudanar da ganawar sirri da shugaban kasar inda ta ce ba gaskiya ba ne, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Mahajjaciya daga Najeriya ta riga mu gidan gaskiya a Saudiyya

Rahoton da ake yadawa ya ce ofishin Netanyahu ya ce Firayim ministan ya kai ziyara UAE a lokacin yakin Iran, inda ya gana da Sheikh Mohammed bin Zayed domin inganta dangantakar kasashen biyu.

Martani na kasar UAE kan ganawa da Netanyahu

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen UAE ta ce dangantakarta da Isra’ila a bayyane take, ba ta ginu kan boyayyun yarjejeniyoyi ko tattaunawar sirri ba.

Sanarwar ma’aikatar ta bayyana cewa duk wata magana game da ziyarar da ba a sanar ba ko yarjejeniya ta boye karya ce.

Ofishin Netanyahu ya bayyana cewa ganawar ta samar da wani babban ci gaba mai tarihi a dangantakar kasashen biyu duk da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Wata majiya ta ce Netanyahu da Sheikh Mohammed sun gana a birnin Al-Ain kusa da iyakar Oman a ranar 26 ga Maris 2026, inda suka dauki sa’o’i.

UAE ta yi magana kan rahoton ganawar sirri da Netanyahu
Fitayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Ziyarar shugaban Mossad a UAE

Majiyar ta kara da cewa shugaban Mossad, Dedi Barnea ya kai akalla ziyara biyu UAE yayin yakin Iran domin hada kai kan ayyukan tsaro da matakan soja.

Rahoton jaridar Euro News ya ce an bayyana cewa Dedi Barnea ne ya kai wadannan ziyara domin tattaunawa kan tsare-tsaren hadin gwiwa.

Kara karanta wannan

Yadda kasar UAE ta rika sakin bama bamai a Iran ta bayan fage

Tun bayan yarjejeniyar Abraham ta shekarar 2020, UAE ta kara kusanci da Amurka da Isra’ila musamman bayan hare-haren da aka kai lokacin yakin Iran.

Jakadan Amurka a Isra’ila Mike Huckabee ya ce Isra’ila ta aika makaman kariya na Iron Dome da jami’anta zuwa UAE lokacin rikicin.

UAE na daga cikin manyan kawayen Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, sannan tana matsayin cibiyar kasuwanci da harkokin kudi mai muhimmanci a duniya.

An yi zanga-zangar kin jinin Netanyahu

A baya, an ji cewa yan Isra’ilada dama sun gudanar da zanga-zanga a Tel Aviv domin nuna adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu a kasar.

Wani dattijo mai shekaru 83 mai suna David Alkan ya bayyana cewa rabuwar kawuna a cikin Isra’ila ta fi zama barazana ga kasar fiye da Iran.

Masu zanga-zangar sun rika dauke da alluna masu rubuce-rubuce kamar “Dakatar da kisan kare dangi” da “Bibi Escobar” domin sukar Netanyahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.