Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

  • Gwamnatin jihar Kano za ta cika alkawarin da tayi wajen ganin an yi adalci a shari’ar Hanifa
  • Mai girma Gwamna zai sa hannu domin a rataye wadanda kotu ta samu da laifin kashe ‘yar yarinyar
  • Kwamishinan shari’a yace sam Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai dauki lamarin da wasa ba

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da a shirye take domin ganin an yi adalci ga malamin makarantar nan, Abdulmalik Tanko da ya yi kisa.

Rahoton The Guardian ya nuna Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a shirye yake domin ganin an tabbatar da adalci ga masu laifin kisan.

Babban lauyan gwamnatin Kano, Musa Lawan ya bayyana cewa wasu suna tunanin ba za a hukunta wadanda aka samu da laifin kashe Hanifa ba.

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

A kwanakin baya aka ji ana zargin wasu mutane da laifin hallaka karamar yarinya mai shekara 5. A watan Yuli ne aka tabbatar masu da laifinsu.

A ranar Alhamis, Musa Lawan ya shaidawa mutanen Kano cewa wadanda aka yankewa hukunci za su dandana kudarsu, akasin tsoron wasu.

Wa'adin kwanaki 90

Kwamishinan shari’an yake cewa hukumar gidan gyaran hali za ta bada shaidar tabbatar da hukunci, wanda zai fito bayan wa’adin daukaka kara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Akwai kwanaki 90 da doka ta ba wadanda ake kara da nufin su daukaka shari’a idan ba su gamsu da hukuncin da Alkalin kotun tarayya ya zantar ba.

Idan ba a daukaka kara ba, gwamna zai sa hannu, idan kuwa an koma kotu, za a saurari shari’a.

Abin da AG yake fada

“Kotu ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wadanda ake tuhuma, kuma gwamna ya yi alkawari zai sa hannu a zartar da hukuncin kisa.

Kara karanta wannan

Rashin Kudi Ya Jawo Gwamnoni Sun Ce A Kori Ma’aikata, a Tsuke Bakin Aljihu Kyam

Saboda haka za mu jira na tsawon kwanaki 90 na lokacin daukaka kara, kafin mu dauki mataki.”
“Idan za a tuna, lokacin da aka fara wannan shari’a, mun yi alkawarin za mu karkare shari’ar, tare da ganin an yi maza-maza wajen zartar da hukunci.”
“Ina tabbatarwa mutane cewa za mu dauki shari’ar da muhimmanci da abin da ya kamata.” - Musa Lawan.

Madadin Hanifa

Kwanakin baya kun ji labari wani Bawan Allah mai suna Abdullahi Ahmed Latus ya ce idan iyayen Hanifa sun yarda, to zai ba su kyautar yarinyar cikinsa.

Wannan mutumi da ke zaune a garin Darazo a jihar Bauchi, ya samu labarin kisan gillar Hanifa, don haka ya jajantawa iyayenta a kan rashin da suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel