Gwamna Makinde Ya Manta da PDP, Zai Yi Takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar Hadaka

Gwamna Makinde Ya Manta da PDP, Zai Yi Takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar Hadaka

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ayyana shirinsa na neman takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027
  • Makinde wanda dan jam'iyyar PDP ne ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar a wata jam'iyya daban saboda rikice-rikicen cikin gida
  • Gwamnan ya sanar da takararsa ne a wani gangami da aka gudanar a dakin taro na Mapo da ke Ibadan yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya tabbatar da shirinsa na neman kujerar shugaban kasa a zaben 2027 da ake tunkara.

Gwamna Makinde ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben a karkashin wata jam'iyya daban ba PDP ba.

Gwamna Makinde zai yi takara a APM
Gwamna Seyi Makinde na Oyo yayin sanar da takarar shugaban kasa a Ibadan. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Makinde ya sanar da hakan ne yayin wani gangamin siyasa da aka gudanar a dandalin Mapo Hall da ke birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tsohon IGP, Usman Baba, ya janye daga neman takarar gwamnan Yobe a APC, ya fadi dalili

Gwamna Bala ya bar PDP zuwa jam'iyyar APM

Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan amininsa, Gwamna Bala Mohammaed na jihar Bauchi ya shiga jam'iyyar.

Gwamna Bala ya tabbatar da barin PDP gaba daya tare da tabbatar da yankan katin jam'iyyar inda ya sanar da yin takara karkashin inuwarta.

Hakan ya biyo bayan rikice-rikicen cikin gida da ya addabi PDP wanda ya tilasta mambobinta da jiga-jiganta da dama barinta.

Gwamna Makinde zai yi takara a APM

Ya bayyana sunansa a hukumance a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APM mai adawa a Najeriya.

Sanarwar ta zo ne yayin da ake ci gaba da samun sauye-sauyen siyasa da hadakar jam’iyyu a jihar Oyo gabanin zaben shekarar 2027.

Tun da farko, Makinde ya jagoranci bangaren Taminu Turaki na PDP wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da jam’iyyar APM.

Rahotanni sun nuna cewa an kulla kawancen ne domin hada kai a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da jihohi masu zuwa.

Kara karanta wannan

NDC: Jam'iyyar su Kwankwaso ta fitar da kudin fom din takarar 2027

Makinde da shugaban jam’iyyar APM na kasa, Yusuf Dantalle, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin bangarorinsu daban-daban.

A karkashin yarjejeniyar, ana sa ran ‘yan takarar bangaren PDP da ke kawance da Makinde za su tsaya takara ne karkashin APM.

Wannan ci gaba ya kara jawo hankalin jama’a da masu sharhi kan siyasa kan yadda zaben shekarar 2027 zai kasance a Najeriya.

Masana siyasa na ganin wannan hadaka tsakanin wasu bangarorin PDP da APM na iya sauya yanayin siyasar jihar Oyo da kasa baki daya.

Hayatu-Deen ya sayi fom din takara a ADC

Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta samu wanda ya fara sayen fom din neman takarar shugaban kasa a karkashinta.

Mohammed Hayatudeen ya sayi fom din jam'iyyar ADC domin neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Mai neman tsayawa takarar shugaban kasar ya bayyana shirye-shiryen da yake da su domin kawo ci gaba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.