Har gara 2015: Kasar nan na cikin ha’ula’i, ba a ga komai ba sai 2023 inji Sanusi II

Har gara 2015: Kasar nan na cikin ha’ula’i, ba a ga komai ba sai 2023 inji Sanusi II

  • Muhammadu Sanusi II ya halarci wani taro da Gidauniyar Akinjide Adeosun ta shirya a Legas
  • Tsohon Sarkin na Kano yace Najeriya na cikin matsala, ya hango irin halin da za a shiga a 2023
  • Masanin yace muddin babu kudin da za a biya bashi a irin wannan yanayi, ana cikin matsala

Lagos - Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da tattalin arzikin Najeriya, yace kasar na cikin halin da ya fi na 2015 muni.

This Day ta rahoto Khalifan na mabiya darikar Tijjaniya ya yi jawabi a wajen bikin da AAF ta shirya jiya, yace lamarin zai iya kara tabarbarewa a 2023.

Gidauniyar Akinjide Adeosun tayi wani taro a kan shugabanci domin a tuna da Akinjide Adeosun wanda shi ne wanda ya kafa gidauniyar.

A matsayin babban bako a taron na Legas, Muhammadu Sanusi II yace ya kamata kowa ya damu da tsaro, talauci, hauhawar farashi da darajar Naira.

Mai na tashi, ana kuka a Najeriya

“Wannan ce kurum kasa mai arzikin mai da ke kuka a lokacin da farashin mai ya tashi a Duniya a sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhammadu Sanusi II
Muhammadu Sanusi II da Sarkin Zazzau Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter
Mun burma rami mai zurfi a 2015, tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu muka cigaba da hakawa kan mu wani ramin da ya fi zurfi.”

- Muhammadu Sanusi II

Masanin tattalin arzikin ya nuna masu mulki sun gaza idan ba a iya biyan bashi. Vanguard ta ce Khalifa yana tir da yadda aka rasa shugabanni masu tunani.

“Mun yi tunani mun shiga babbar matsala a 2015. Amma 2015 ba komai ba ne idan aka kamanta da abin da zai faru a 2023.

Mu na fama da ta’addanci, rikicin ‘yan bindiga, hauhawar farashi, matsalar farashin kudin kasar waje da ke sama da kasa.
Abin da ya fi muni shi ne wadanda ke shugabanci suna sa ran za muyi masu godiya bayan sun bar ofis.” - Muhammadu Sanusi II.

Shawarar Gwamnoni

Dazu mu ka samu rahoto Gwamnonin Najeriya sun ba gwamnatin tarayya shawara ta kori ma’aikatan da suka kai shekara 50 saboda rashin kudi.

An bada shawarar janye tallafin man fetur, sannan a ruguza SIP tare da rage kudin kwangilolin ‘Yan majalisa, duk saboda a fita daga matsin lamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel