ImpeachBuhariNow: Yadda Ma'abota Facebook Ke Goyon bayan tsige Shugaban Najeriya

ImpeachBuhariNow: Yadda Ma'abota Facebook Ke Goyon bayan tsige Shugaban Najeriya

  • Wasu daga cikin masu amfani da dandalin Facebook sun karbi kiran tsige shugaban kasa a Najeriya
  • Abba Hikima ya kawo batun #ImpeachBuhariNow, mutane da-dama sun yi tarayya da shi a kan haka
  • Mafi yawan masu magana sun gamsu a tunbuke Muhammadu Buhari saboda matsalar rashin tsaro a kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022, Lauyan nan mai tashe a Kano, Abba Hikima Esq. ya nuna cikakkiyar goyon bayansa na tsige shugaban kasa.

“Ni, Abba Hikima Esq, namiji, baligi, Musulmi, dan Nigeria, yaren Hausa, ina goyon bayan matakin Majalisar Tarayya na tumbuke Shugaba Buhari a watan Satumba mai zuwa saboda gazawar sa wajen tsare rayukan mu. #ImpeachBuhariNow”

Da yake karin bayani, Hikima ya jero amfanin majalisa ta tsige shugaban kasar, yace hakan zai zama misali ga shugabannin da za ayi nan gaba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa fitaccen tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya rasuwa

Lauyan yace hakan zai nuna riƙar dimukradiyya, sannan zai ƙara ƙarfafa gwiwar ‘yan majalisa, tare da sa ran samun saukin rashin tsaro da ya ta’azzara.

Bayan nan aka ji Ibrahim Waziri yana cewa ya yi na’am da kiran Sanatocin. Kwararren marubucin yace tun tuni ya so a rika zanga-zanga domin nuna fushi.

Ni, Abdulaziz T. Bako, MBBS, MPH, PhD, namiji, baligi, Musulmi, dan Nigeria, yaren Hausa, ina goyon bayan matakin Majalisar Tarayya na tumbuke Shugaban kasa Manjo Janar Buhari a watan Satumba mai zuwa saboda gazawar sa wajen tsare rayukan mu. #ImpeachBuhariNow

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Inji Abdulaziz Tijjani wanda kwararren Likita ne da ke ganin an gaza tsare rayukan al’umma.

Wani ‘dan jarida ya nuna yana goyon bayan a sauke shugaba Muhammau Buhari daga mulki.

Ni Aliyu Jalal,

Namiji mai jini a jika,

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

Baligi mai cikkaken gemu,

Musulmi na kwarai amma sai yawan yin vawulence,

Dan Nigeria mai cikkaken iko,

Kabilar Kanuri amma yaren Hausa,

Ina goyon bayan matakin Majalisar Tarayya na tumbuke Shugaba Buhari a watan Satumba mai zuwa saboda gazawar sa wajen tsare rayukan mu da dukiyoyinmu.

#ImpeachBuhariNow

Shugaban Najeriya
Mai girma Shugaban kasa Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

"Ko kwana daya ya rage, a sauke shi"

Ko da kwana ɗaya ya rage shugaba Buhari ya kammala wa'adin mulkinsa, ina goyon bayan yan majalisa su tsige shi daga kan muƙamin sa na shugaban kasa,saboda matsalolin da muke fama da su a Najeriya sun wuce a zuba ido a yi shiru. #ImpeachBuhariNow

- M.A Aliyu.

Ni, Abdulrahman Yunusa, namiji, baligi, Musulmi, cikakken ɗan Nigeria kuma yaren Kare-Kare - Hausa, Ina goyon bayan matakin Majalisar Tarayya na tumɓuke/tsige Shugaban ƙasa Buhari a watan Satumba mai zuwa saboda gazawarsa wajen tsare rayuka da dukiyoyin al'umma.

#ImpeachBuhariNow

- Abdulrahman Yunusa

Ga abin da Sadiq Albani ya rubuta a shafinsa:

Kara karanta wannan

Allah ya bada sa’a: Fitaccen Farfesa Yana Goyon Bayan Tsige Buhari da Gwamnoni

Ni, Sadiq Albani, namiji, baligi, Musulmi, dan Nigeria, yaren fulani, ina goyon bayan matakin Majalisar Tarayya na tumbuke Shugaba Buhari a watan Satumba mai zuwa saboda gazawar sa wajen tsare rayukan mu.

#ImpeachBuhariNow

Abubakar Yusuf Gama ya yi gatse ne, yana cewa: “Tsoho mai farin jini, ya hau ana murna, zai sauka ma ana murna.”

#ImpeachBuhariNow

Mubarak Ibrahim ya yi dogon sharhi a kan tsadar rayuwa da matsalar tsaro, a karshe ya nuna yana tare da masu cewa #ImpeachBuhariNow.

In ma yaudarar mutane ƴan majalisa su ke yi a kan maganar cire shi to mu da gaske mu ke! Da mu zauna ƙarƙashin mulkin zalunci gwanda mu koma ƙarƙashin mulkin pastor mai tausayi. Koma dai me zai kasance, kuma koma waye zai yi riƙon ƙwaryar, to tabbas ya fi Buharin da ba ya komai sai kallo-kallo a ɗaki da kuma yawon biranen Turai da na Afirka.
Mun faɗa mun ƙara, #ImpeachBuhariNow

Kara karanta wannan

Mafi Yawan Sanatoci Sun Yi Na’am da Yunkurin Tunbuke Buhari Inji Sanatan Bauchi

- Mubarak Ibrahim Lawal!

Wani malamin jami’a, Dr. Ameer Abdulaziz yace baya ga goyon bayan tsige shugaban kasa, yana kiran a dawo da duk Sanatan da bai goyon bayan wannan kudiri.

Wata Baiwar Allah, Injiniya Naimah Ibrahim Imam tana cikin masu na’am da wannan batu:

Ni, Na'imah Ibrahim Imam( Bsc. Pet&gas engineering), ta mace, mai kishin kasa, Musulma, yar Nigeria, Bahaushiya, Ina goyon bayan matakin Majalisar Tarayya na tumbuke Shugaba Buhari a watan Satumba mai zuwa saboda gazawar sa wajen tsare rayukan mu da Kuma tsaida yajin aikin ASUU. #ImpeachBuhariNow

- Naimah Ibrahim Imam

Shi kuwa Rabi'u Ahmad Sokoto ya bada labarin halin rashin tsaro da mutanensa suka shiga, yace don haka ya shiga sahun masu goyon bayan ayi waje da shugaban kasar.

Dr. Marzuq Ungogo wani Likitan dabbobi a Birtaniya kuwa cewa ya yi:

Ya isheka darasi yadda mutanen da suka tsine mana a 2016 a kan Buhari, su ne su ke kira da a tsige shi a 2022. Mu lokacin ma ‘Baba gyara kayanka’ kawai muka ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel