An Gindaya Sharuda Kafin Cigaba da Karatu a Kwalejin da aka Kashe Deborah

An Gindaya Sharuda Kafin Cigaba da Karatu a Kwalejin da aka Kashe Deborah

  • A mako mai zuwa za a bude Kwalejin ilmi na Shehu Shagari domin dalibai su cigaba da karatu
  • Wannan ya biyo bayan kusan watanni uku da aka yi makarantar tana rufe saboda an yi batanci
  • Kowane dalibi zai biya kudi kafin ya cigaba da daukar karatu a makarantar da ke garin Sokoto

Sokoto - Za a bude kwalejin ilmi na Shehu Shagari da ke garin Sokoto biyo bayan rikicin da ya faru a watan Mayu, inda aka hallaka Deborah Yakubu.

Premium Times ta fitar da rahoto a ranar 5 ga watan Agusta 2022 da yace an yi na’am da a sake bude wannan makarantar horas da malamai da ke Sokoto.

Tun da aka babbaka Deborah Yakubu a sakamakon kalaman batanci da tayi a dandalin WhatsApp, ama bada umarnin a rufe wannan makaranta.

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

A ranar 8 ga watan Agusta 2022 wanda zai kama Litinin za a koma daukar darasi a SSCOE. Mahukuntar kwalejin ilmin ne suka bada wannan sanarwa.

Magatakardar kwalejin da ke jihar Sokoto, Gandi Asara ya tabbatar da cewa majalisar da ke kula da makarantar ta amince a koma aiki a mako mai zuwa.

Hukumar kwalejin ta sanar da dalibai za su biya N1000, sannan za su yi rantsuwar cewa za su zama masu hali na kwarai yayin karatunsu a makaratar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Deborah
Marigayiya Deborah Samuel Yakubu Hoto: Tribune
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci hukumar makarantar ta zo da wannan tsari ne domin gudun irin haka ta sake faruwa, har a kai ga sanadiyyar dukiya ko rayuka.

Sai kowane dalibi ya biya wannan kudi, ya kuma sa hannu a takardar rantsuwa sannan zai dawo.

Gwamna ya bada umarnin gaggawa

Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci shugabannin kwalejin suyi gaggawar tsaida rana domin dalibai su cigaba da karatunsu.

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Gwamnan ya fitar da jawabi ta bakin hadiminsa, Muhammad Bello, ya na mai tabbatar da zai dabbaka shawarwarin da kwamitin da ya kafa suka bada.

Bayan abin ya faru, an kafa wani kwamitin mutane 12 da ya yi bincike a kan kisan Daborah Yakubu mai shekara 22, da nufin kawo matakin zaman lafiya.

Fasto ya kawo agaji

An taba samun labari cewa wani babban malamin coci ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin iyayen Deborah Samuel, da kuma ragowar 'ya'yan su baki ɗaya.

Fastor Chibuzor Chinyere yace zai ɗauki nauyin 'yan uwan Deborah, sannan ya ba iyayenta aikin yi. Faston yana son ganin duk sun daina wahala a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel