Bayan Shekaru 11 Yana Zuwa Ofis, Kotu tace Ya Maido Duka Albashin da Aka Biya Shi

Bayan Shekaru 11 Yana Zuwa Ofis, Kotu tace Ya Maido Duka Albashin da Aka Biya Shi

  • Lauyoyin ICPC sun yi galaba a kan wani Muhammed Nasiru da suka kai kara a kotun garin Jos
  • Hukumar ICPC ta zargi tsohon ma’aikacin da karbar albashi ba tare da ya cancanci mukamin ba
  • A karshe Alkali tace a dawo da kudin da aka biya shi, sannan ta yanke masa dauri a gidan maza

Plateau - Wani babban ma’aikaci a National Veterinary Research Institute da ke garin Vom a Filato zai dawo da albashin da ya rika karba.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Juma’a cewa jami’in da ke aiki a ma’aikatar NVRI da ke binciken lafiyar dabbobi ya sha kashi a kotu.

Babban kotun jiha da ke garin Jos ya umarci Muhammed Nasiru ya maido albashin da ya karba a matsayin babban ma’aikacin NVRI.

Rahoton da aka fitar a ranar 5 ga watan Agusta 2022 ya tabbatar da Alkalin kotun jihar ya zartar da hukuncin dauri a kan Mista Nasiru.

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Zargin da ke wuyan Muhammed Nasiru

ICPC mai yaki da rashin gaskiya ta maka Muhammed Nasiru a kotu bisa zargin laifuffuka biyu, a makon nan aka zo karshen shari’ar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotu ta yanke masa wannan hukunci saboda ya yi karya game da takardunsa, kuma ya gagara gamsar da kuliya kan daukarsa aiki da aka yi.

National Veterinary Research Institute
Dakin bincike a National Veterinary Research Institute Hoto: commonwealthofnations
Asali: Facebook

Hukumar ICPC da ta shigar da karar tsohon ma’aikacin tayi nasara wajen daure shi na tsawon watanni shida a gidan gyaran hali a Najeriya.

Lauyoyin ICPC sun fadawa kotu cewa Nasiru bai dace ya dare kujerar da ya rike ba saboda an yi masa ritayar dole daga aiki tun shekarar 2003.

Kamar yadda lauyoyi suka shaidawa Alkali Christy Dabup, hukumar NJI ta kasa da ke garin Abuja tayi wa Nasiru ritaya shekaru 20 da suka wuce.

Kara karanta wannan

Muna Bukatar Shirin Da Zai Sa Mu Gaba Da Yan Ta’adda – Osinbajo Ya Fadawa Sojoji

Bayan an sallami tsohon ma’aikacin daga aiki, sai ga shi ya kai matsayin babban jami’in da ke kula da daukar aiki a ma’aikatar tarayyar ta Vom.

Leadership ta bayyana cewa Mai shari’a Dabup ta ba wanda ake kara damar biyan tarar N150, 000 a madadin ya yi watanni shida a gidan maza.

KASTELEA a Kaduna

Shekaru kusan shida da suka wuce aka kirkiro da KASTELEA. A jiya aka ji labari jami’an hukumar sun taba cafke har da yaron Gwamnan Kaduna.

Bashir El-Rufai ya shaida cewa da aka yi ram da shi a cikin mota a kan titi, ya biya tarar kudin da aka lafta masa, a maimakon nuna shi ‘dan wani ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel