'54 Suna Asibiti, 4 Sun Rasu': Halin da Mahajjatan Najeriya Suke ciki a Saudiyya
- Hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa mahajjata Najeriya 54 na kwance a asibitocin Saudiyya yayin da ake gudanar da aikin Hajjin 2026
- Mahajjata hudu mata sun rasu sakamakon matsalolin zuciya da wasu cututtuka yayin gudanar da ibadar Hajji a Saudiyya
- Likitoci da jami’an lafiya 287 daga Najeriya na kula da lafiyar mahajjata a Makkah da Madinah duk da matsin aiki da suke fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Saudiyya - Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cewa akalla mahajjatan Najeriya 54 ne ke kwance a asibitoci a kasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Shugaban tawagar likitocin Najeriya ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan lafiyar mahajjatan Najeriya da ke birnin Makkah.

Source: UGC
Asibitoci 5 da Najeriya ke amfani da su
Dr. Ibrahim Abubakar, ya ce hukumar ta samar da asibitoci guda biyar da hukumomin Saudiyya suka amince da su domin kula da lafiyar mahajjata, in ji rahoton Daily Trust.
A cewarsa, akwai asibitoci biyu a Madinah da kuma guda uku a Makkah domin ba da kulawar lafiya ga mahajjatan Najeriya.
Ya bayyana cewa an fara aikin kula da lafiyar mahajjatan ne tun bayan isa Saudiyya ranar 28 ga watan Afrilu, bayan samun amincewa da lasisi daga hukumomin kasar.
Jami’in ya ce sababbin dokokin Saudiyya sun hana bude kananan cibiyoyin jinya kamar yadda ake yi a baya, lamarin da ya sa duk marasa lafiya ke tururuwa zuwa manyan asibitocin hukumar.
A cewarsa, hakan ya kara matsin aiki ga jami’an lafiya saboda yawaitar marasa lafiya da ke neman magani.
An tura mahajjan Najeriya asibitocin Saudiyya
Tawagar likitocin ta ce an tura sama da mahajjata 24 zuwa asibitocin Saudiyya daga Madinah, yayin da aka tura fiye 35 daga Makkah.
An ce mafi yawan wadanda aka tura sun fito ne daga asibitin Misfalah wanda ke kula da mahajjata daga kusan jihohi 19 na Najeriya.

Kara karanta wannan
Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya
Jami’an sun bayyana cewa ana mika marasa lafiya masu bukatar kulawa ta musamman ko ta gaggawa zuwa manyan asibitoci kamar asibitin King Abdulaziz ta hanyar jami’an agajin gaggawa na Saudiyya.
Mahajjata 4 sun rasu a kasar Saudi
Hukumar ta kuma tabbatar da rasuwar mahajjata hudu ‘yan Najeriya, inda dukkansu mata ne, in ji rahoton Leadership.

Source: Facebook
Shugaban tawagar likitocin ya ce mafi yawan wadanda suka rasu sun mutu ne sakamakon matsalolin zuciya, ciki har da bugun zuciya da ciwon zuciya mai tsanani.
A cewarsa, tsananin zafi, gajiyar ibada da kuma wasu cututtuka da mahajjata ke dauke da su tun kafin tafiya na daga cikin abubuwan da suka haddasa matsalolin.
Jami’an lafiya sun ce sun sha wayar da kan mahajjata kan muhimmancin gujewa yawan yawo a lokacin tsananin zafi da kuma yawaita shan ruwa domin kare lafiyarsu.
2026: Maniyyaciya daga Najeriya ta rasu
A wani labari, mun ruwaito cewa, wata maniyyaciya ƴar shekara 73 daga Adamawa, Mallama Aishatu Muhammadu, ta rasu a hanyarta ta zuwa Madina.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa ciwon zuciya ne ya yi sanadin mutuwar tata yayin da take cikin tafiya daga birnin Jeddah.
Shugaban NAHCON ya jajanta wa iyalan mamaciyar tare da ba su tabbacin dawo masu da dukkan kayayyakin da ta bari a ƙasa mai tsarki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
