Jiragen Kasan Legas-Kano da Ajaokuta Sun Daina Aiki Bayan Harbin wasu Fasinjoji

Jiragen Kasan Legas-Kano da Ajaokuta Sun Daina Aiki Bayan Harbin wasu Fasinjoji

  • Shugaban NRC mai kula da harkokin jirgin kasa a Najeriya yace jirgin Kano-Legas ya daina aiki
  • Akwai matsalar tsaro a yankunan Kaduna da Minna, don haka aka dakatar da aikin jiragen
  • Haka zalika NRC ta tabbatar da cewa jirgin Warri-Itakpe ba zai rika tsayawa a Ajaokuta ba

Abuja - Hukumar NRC mai kula da harkokin jirgin kasa a Najeriya ta dakatar da ayyukan jiragen kasan Legas zuwa Kano da kuma jirgin Ajaokuta.

Tribune ta kawo rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta 2022 cewa NRC ta dauki wannan mataki a madadin gwamnati saboda matsalar rashin tsaro.

Majiyoyi da dama daga hukumar ta NRC sun shaidawa manema labarai cewa an dakatar da aikin jirgin Ajaokuta a dalilin harin da aka kai wa wasu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi shugaban 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

A ranar Litinin da ta wuce aka samu ‘yan bindiga sun aukawa fasinjoji a yankin Warri-Itakpe.

Haka zalika rashin tsaron ya yi sanadiyyar daina aikin jiragen kasan Legas zuwa Kano. A dalilin haka aka daina amfani da jiragen Kaduna zuwa Abuja.

Rahoton Punch ya nuna ba za a dawo aiki ba har sai lokacin da aka iya tabbatar za a iya kare lafiyar ma’aikata da fasinjojin da ke bi ta wadannan hanyoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiragen Kasan Legas-Kano
Wani Jirgin kasa a Najeriya Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Babbar Darektan NRC na kasa, Fidet Okhiria ya tabbatarwa manema labarai cewa jiragen Legas zuwa Kano da na Ajaokuta sun daina aiki a halin yanzu.

Da yake magana game da Warri-Itakpe, Fidet Okhiria ya shaida cewa ba za su dakatar da aiki a hanyar ba, sai dai ba za a rika dakatawa a Ajaokuta ba.

“Dalili kuwa shi ne a jiya (Litinin), yayin da wasu fasinjoji suke barin tashar jirgi a motocinsu, sai aka samu mutane sun buda masu wuta.

Kara karanta wannan

Dakile rashin tsaro a babban birnin tarayya: IGP ya umarci a zagaye Abuja da tulin jami'an tsaro

Saboda haka sai muka ce ba za mu sake tsayawa a nan ba (tashar Ajaokuta) saboda fasinjoji.”

- Fidet Okhiria

Akwai matsala a hanyar Kaduna/Neja

A bayanin da yayi a ranar Talata, shugaban NRC yace jirgin Warri-Itakpe yana aiki, amma babu maganar a tsaya a Ajaokuta saboda halin da ake ciki a yau.

Baya ga jirgin Legas zuwa Kano, babu wani jirgin kasa da ba ya aiki. Dalilin dakatar da aikin jiragen shi ne matsalar rashin tsaro a yankin Minna da Kaduna.

Tare jirgin Kaduna - Abuja

A watan Maris ku ka samu labari Rotimi Amaechi, a lokacin yana Ministan sufuri, yace ya yi hasashen harin da aka kai wa jirgin kasan Kaduna-Abuja.

Rotimi Amaechi yace tun farko sai da ya bukaci a kashe N3bn wajen sayan wasu kayan tsaro, rashin tanadar wadannan kayan aiki ya jawo matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel