Yadda Tinubu Ya Titsiye Shugaban Ma’aikatansa game da Zargin Tsige Kakakin Majalisa

Yadda Tinubu Ya Titsiye Shugaban Ma’aikatansa game da Zargin Tsige Kakakin Majalisa

  • Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa rikicin siyasar Lagos ya kusa shafar aikinsa
  • Gbajabiamila ya ce tsige tsohon kakakin majalisar Lagos, Mudashiru Obasa, ya kusa haddasa masa rigima da mai gidansa, Bola Tinubu
  • Ya ce Tinubu ya tambaye shi ko yaronsa na cikin masu haddasa rikicin majalisar Lagos bayan bayanan sirri sun danganta sunansa da lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya bayyana yadda ya kusa rasa mukaminsa.

Gbajabiamila ya bayyana yadda rikicin tsige tsohon kakakin majalisar Lagos, Mudashiru Obasa ya jefa shi cikin matsala a shekarar bara.

Yadda Gbajabiamila ya kusa rasa mukaminsa
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da Bola Tinubu. Hoto: Femi Gbajabiamila.
Source: Facebook

Abin da Tinubu ya ce ga Gbajabiamila

Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya kira shi zuwa gidansa da ke Abuja domin tambayarsa ko Desmond Elliott na daga cikin mutanen da ke haddasa rikicin, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

Gbajabiamila ya ce ya tabbatar wa shugaban kasa cewa Desmond Elliott yaronsa ne kuma bai yi imanin yana cikin masu tayar da rikicin ba.

Sai dai shugaban kasa ya ce bayanan sirri da ya samu sun nuna cewa dan majalisar na da hannu a rikicin majalisar dokokin jihar Lagos.

Bayan ganawar, Gbajabiamila ya ce ya tuntubi Desmond Elliott tare da gargadinsa ya fice daga cikinsu wadanda ake zargi idan har yana da hannu a lamarin.

Ya bayyana cewa bayan kwanaki uku, babban daraktan DSS ya tuntube shi yana sanar da cewa ana alakanta sunansa da yunkurin tsige Obasa.

Tinubu ya titsiye Gbajabiamila kan rikicin Lagos
Shugaba Bola Tinubu yayin jawabi a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Gbajabiamila ya janye goyon bayansa ga Ellliot

A cewarsa, jami’an tsaro sun yi zargin cewa yana goyon bayan Desmond Elliott wajen haddasa rikicin siyasar majalisar dokokin Lagos.

Ya ce:

"Na kusa rasa aikina na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ga Shugaba Tinubu a shekarar da ta gabata. Shugaba Tinubu ya kira ni zuwa ofishinsa na sirri a gidansa da ke Abuja yayin rikicin tsige Obasa, ya tambaye ni ko Desmond Elliott yaro ne. Na amsa wa shugaban cewa eh, yaro na ne."

Kara karanta wannan

Maniyyatan Jigawa sun gamu da matsala a Saudiyya, barayi sun masu tas a Makkah

Gbajabiamila ya ce ya sake tuntubar Desmond Elliott domin ya fito fili ya musanta hannu a rikicin domin kare sunansa daga zarge-zargen, cewar The Guardian.

Sai dai ya ce har zuwa yanzu, Desmond Elliott bai fitar da wata sanarwa a bainar jama’a domin musanta hannu a rikicin ba wanda ya dauki lokaci mai tsawo.

Rahotanni sun bayyana cewa Gbajabiamila ya janye goyon bayansa ga Desmond Elliott wanda ke neman wa’adi na hudu a majalisar dokokin Lagos.

Gbajabiamila ya roki Arewa su zabi Tinubu

A baya, kun samu labarin cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya bukaci shugabannin Arewa su mara wa Bola Tinubu baya.

Gbajabiamila ya bayyana irin kokari da Tinubu ke yi na hada kan Najeriya inda ya ce ya cancanci goyon bayan yan yankin saboda abubuwan alheri da ya yi masu.

Hakan ya biyo bayan samun goyon baya da Tinubu ke kara samu a jihohi da dama da ke Arewacin Najeriya yayin da ake shirin gudanar da zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.