Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
A kullun garkuwar jikin dan adam cikin bautuwa take domin ganin ta hallaka kwayoyin cututtukan da ke yiwa jikin dan adam kawanya. Duk da karfin da wannan garkuwar jiki ke da shi, ta na bukatar tallafi ta bangaren abinci.
A jiya ne akayi badakala a wurin addu’ar Fidau ta 8 ga mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Buba Jibril, a Lokoja, jihar Kogi, inda kungiyar kato da gora suka hana hukumar SARS su kama Sanata Dino Melaye na Kogi.
Hukumar aikin hajji ta NAHCON, ta jihar Kaduna, ta bukaci masu niyya dasu cigaba da biyan kudin tafiya aikin hajjin bana. Jami’in kula da harkokin jama’a na hukumar Yunusa ya bayyana cewa an shawarci mutane dasu cigaba da biya.
Idan kanaso ka kara lafiya ka zama bakada matsala a jikinka, ka samu karfi, zogala shine maganin da zaya maka wadannan abubuwa. Zogala ya kasance iccen gado a kasar Afrika ta Kudu, saboda suna amfani dashi a la’adance.
Wasu ‘yan kungiya dake kiran kasu da Adalci Buhari SAK,wanda tsohon gwamnan jihar Sokoto Dahiru Yusuf Yabo, sunyi ikirarin cewa ‘yan APC ne suke kokarin bata masu suna a jihar ta Sokoto saboda adawa dake tsakaninsu.
Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya nuna alhini kan mutuwar Sanata mai wakiltan Katsina ta Arewa, Sanata Mustapha Bukar a ranar Laraba, bayan yayi yar gajeriyar rashin lafiya a birnin tarayya, Abuja.
Yarinyar da kakarta ta Konawa hannuwa, anyi mata aiki don a gyara illolin da kunar tayiwa hannuwan. Idan ba’a mance ba yarinyar wadda ake kira da Hope, kakar tata ta kona mata hannuwa ta hanyar dora hannuwan bisa risho.
Agu ya samu dama ne bayan sirikinsa fasto wanda yarinyar ke yiwa aiki yayi tafiya a cikin shekarar 2017. Rahoto yazo cewa wata makwabciyarsu ce ta lura da kumburin cikin yarinyar kafin ta sanar da Faston da matarsa.
Ben Murray-Bruce, Sanata mai wakiltan Bayelsa ta yamma ya caccaki kakakin shugaban kasa, Garba Shehu kan kiran yan Najeriya da yayi da malalata. Garba Shehu yace yan Najeriya masu lalaci ne kadai ke korafin yunwa.
Aisha Musa
Samu kari